Garkuwa: Yadda makarantu, wuraren ibada da masu sufuri suka tsaurara matakan tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Makarantu, coci-coci da masu gudanar da harkokin sufuri a wasu sassan Nijeriya sun ƙara tsaurara matakan tsaro, sakamakon ƙara fargabar hare-haren ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Wasu makarantu sun ƙara ɗaukar matakan kariya, ciki har da saka kyamarorin sa ido, ƙarfafa katangar makarantu, ƙara yawan jami’an tsaro da kuma samar da hanyoyin tserewa idan aka samu aukuwar wani hari.

ɗaukar wazannan matakai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa makarantu da sauran wuraren da ake ganin suna da rauni a faɗin ƙasar.

Gwamnatin Tarayya ita ma na ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa Shirin Samar da Tsaron Makarantu tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

Mataimakin Shugaban ƙungiyar Malaman Nijeriya (NUT), Bashir Oyewo, ya ce ƙungiyar na aiki tare da gwamnati da hukumomin tsaro domin inganta tsaron malamai da ɗalibai, musamman waɗanda ke zaune da karatu a yankunan karkara.

Wani shugaban makaranta a Ikorodu, Jihar Legas, ya bayyana cewa an samar da wata ƙofa ta ƙarin kariya da kuma hanyar tserewa a cikin harabar makarantar, domin bai wa ɗalibai da ma’aikata wata hanyar fita idan aka samu aukuwar gaggawa.

Shugaban makarantar ya ƙara da cewa an wayar da kan ɗalibai kan yadda za su yi amfani da hanyar tserewar tare da taimaka wa junansu idan aka kai hari.

ƙungiyoyin Iyaye da Malamai (PTA) su ma na tallafa wa makarantu ta hanyar ɗaukar ƙarin jami’an tsaro, musamman a makarantun da ake ganin tsaron da gwamnati ta samar bai wadatar ba.

Oyewo ya ce, ana kuma ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa Shirin Tsaron Makarantu domin tunkarar sabbin matsalolin tsaro.

Matakan da ake ɗauka a matakin ƙasa sun haɗa da samar da kayayyakin tsaro, shirye-shiryen tunkarar gaggawa da kuma hanyoyin gaggauta kai ɗauki a makarantu.

Makarantu masu zaman kansu a Jihar Osun su ma sun ɗauki matakai daban-daban, ciki har da saka kyamarorin CCTV, ɗaga tsayin katangar makarantu da ɗaukar jami’an tsaron yankin domin ƙara kariya.

Haka kuma, masu harkar sufuri sun fara ɗaukar matakan kariya domin kare direbobi da fasinjoji. Wasu ƙungiyoyin ma’aikatan sufuri sun shawarci mambobinsu da su guji tafiye-tafiyen dare marasa muhimmanci tare da yin taka-tsantsan yayin tafiya.

Sakatare na ƙasa mai Kula da Tsare-tsare na ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Hanya ta Nijeriya (RTEAN), Abdulrahman Onikijipa, ya ce masu harkar sufuri sun ƙara tsaurara binciken tsaro a tashoshin mota da manyan hanyoyin ƙasa.

Ya kuma taɓa yin kira ga masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiyen dare a wuraren da ke da haɗari tare da gaggauta sanar da hukumomin tsaro idan suka lura da wasu abubuwan da ba su dace ba.

A Jihar Oyo kuwa, Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Oyo (OYRTMA) ta ƙara sintiri a kan tituna, inda jami’anta ke sa ido kan abubuwan da ke faruwa tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga hukumomin tsaro.

Matsalar tsaro ta kuma jefa wasu masu shirin shiga Hukumar Kula da Hidimar Matasa ta ƙasa (NYSC) cikin fargaba.

Wasu daga cikin waɗanda suka kammala karatu kuma ke jiran a tura su hidimar ƙasa sun bayyana damuwarsu kan tafiya zuwa jihohin da suke ganin ba su da isasshen tsaro domin gudanar da hidimar wajibi.

Rahotanni sun ce NYSC na nazarin yadda ake tura mambobinta, ciki har da yiwuwar tura wasu ’yan yi wa ƙasa hidima zuwa jihohinsu na asali.

Hukumar na kuma aiki tare da hukumomin tsaro domin ƙara kariya ga ’yan yi wa ƙasa hidima yayin da suke tafiya zuwa wuraren da aka tura su domin gudanar da aikin yi wa ƙasa hidima.

Coci-coci da sauran cibiyoyin addini su ma ba a bar su a baya ba wajen ɗaukar matakan tsaro.

Wasu coci-coci sun sake duba tsarin tsaron da suke amfani da shi tare da ƙara matakan gano da kuma sa ido kan sababbin mambobi.

Wani babban jami’in coci ya ce ana yawan duba matakan tsaro da ake amfani da su, yayin da wasu coci-coci suka fara buƙatar sababbin mambobi su bayyana kansu a yayin ibadu da taruka, a matsayin wani ɓangare na tsarin tsaro.

Matakan da ake ɗauka na nuna yadda makarantu, cibiyoyin addini, ƙungiyoyin sufuri da sauran ƙungiyoyi ke ƙara ƙoƙarin hana hare-hare tare da kare rayuka da dukiyoyi, a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro.

Hukumomi da jama’a na ci gaba da kira ga ’yan Nijeriya da su kasance cikin shiri da taka-tsantsan, tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga hukumomin tsaro da suka dace.

Hukumomin tsaron ƙasa da shugabannin makarantu kuma na ƙara ƙoƙarin inganta tsarin gano barazana tun da wuri, musayar bayanan sirri da kuma gaggauta ɗaukar matakin da ya dace idan aka samu yanayin gaggawa.

By ukarofi

Leave a Reply