
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), ta sanar da ranar 30 ga watan Satumba a matsayin lokacin da za a fara horar da ‘yan rukunin C na 2026.
A wata takarda da Daraktar hulɗa da jama’arta, Caroline Embu ta fitar a ranar Talata, hukumar ta sanar da al’umma musamman ɗaliban rukunin C ɗibar farko cewa za a fara aikin horar da su ne a ranar 30 ga Satumba, sannan a kammala a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026.
Ta kuma ce, yayin da aka fara rajistar ‘yan rukunin a ranar 30 ga Satumba, za a kammala aikin a 2 ga Oktoba, 2026 tare da yin bikin rantsarwa a ranar.
A cewar sanarwar, an tsara aikin bayar da horon ne makonni uku a baki ɗaya jihohi 36 na faɗin Nijeriya da Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja.
Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Olakunle Nafiu ya yi wa waɗanda abin ya shafa fatan alkhairi da zuwa sansanonin da aka tura su cikin ƙoshin lafiya, yana mai kira a gare su da su ƙaurace wa tafiye-tafiyen dare da shiga mota akan hanya a madadin zuwa tashoshin mota a yankunansu.
