Daga AISHA ASAS
Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyar wannan shafi, inda a ‘yan kwanakin nan muke ƙoƙarin duba wasu daga cikin abubuwan da suka shafi kula da fata da kyau, musamman waɗanda ake yawan amfani da su ba tare da cikakken bayani kan illarsu ko amfaninsu ba.
A makon da ya gabata, mun yi magana ne kan wani sinadari da aka daɗe ana amfani da shi a wasu kayayyakin kula da fata, amma wanda ke iya zama mai matuƙar haɗari idan aka yi amfani da shi ba daidai ba, wato mercury.
A wannan makon kuwa, za mu ci gaba da binciken wannan batu na neman ƙarin hasken fata, amma a wannan karon hankalinmu zai koma kan wani sinadari da sunansa ya zama ruwan dare a cikin kayayyakin da ake amfani da su wajen rage duhun wasu sassan fata, wato hydroquinone.
Saidai kafin mu yi gaggawar yanke hukunci a kansa, akwai wata tambaya da ya kamata mu fara yi: Shin hydroquinone da kansa ne matsalar, ko kuwa yadda ake amfani da shi ne ya mayar da shi abin tsoro?
Hydroquinone wani sinadari ne da ake amfani da shi wajen rage launin wasu sassan fata, musamman wuraren da suka yi duhu fiye da sauran sassan jiki. Saboda haka, ba daidai ba ne a ce hydroquinone ba shi da wani amfani a fannin likitanci. A wasu yanayi ana amfani da shi wajen magance matsalolin launin fata, amma amfani da shi yana buƙatar kulawar ƙwararren ma’aikacin lafiya, domin a tantance matsalar da ake son magancewa da kuma yadda ya dace a yi amfani da sinadarin.
To, ina matsalar take?
Matsalar tana iya tasowa ne idan mutum ya ɗauki hydroquinone a matsayin wani man shafawa na yau da kullum da zai iya amfani da shi yadda ya ga dama, ba tare da sanin dalilin da ya sa yake amfani da shi ba, tsawon lokacin da ya kamata ya yi amfani da shi, ko kuma adadin sinadarin da ke cikin samfurin. Wannan ya fi zama abin damuwa idan samfurin da ake amfani da shi ba a tabbatar da ingancinsa ba, ko kuma ba a san ainihin sinadaran da ke cikinsa ba.
A nan ne neman gyara ƙaramin tabo zai iya rikidewa zuwa wata babbar matsala. Domin abin da mutum yake tunanin zai taimaka masa ya daidaita launin fata, idan aka yi amfani da shi ba daidai ba, zai iya haifar da wata matsalar da ba ya tsammani.
Hukumar Abinci da Magunguna ta Amurka, FDA, ta ce ta samu rahotannin matsalolin fata da suka haɗa da kuraje, kumburin fuska da kuma ochronosis daga amfani da wasu kayayyakin haskaka fata masu ɗauke da hydroquinone. Ochronosis wata matsala ce da za ta iya haifar da canjin launin fata mai ɗorewa, musamman idan amfani da sinadarin ya kasance ba tare da kulawar da ta dace ba.
Wannan shi ne abin da ya kamata ya sa mu tsaya mu yi tunani: Mace ta fara amfani da cream ne saboda tana son ta kawar da tabo, ta rage duhun wani sashe na fatar jikinta ko kuma ta daidaita launin fatarta. Amma shin zai yiwu a ƙarshe abin da ta ɗauka domin gyara fatar ya zama shi kansa sanadin wata matsalar launin fata?
A nan ne ya kamata mu fara bambance tsakanin amfani da sinadari a matsayin wani ɓangare na magani ƙarƙashin kulawa, da kuma amfani da shi a matsayin kayan kwalliya kawai saboda ana son fata ta ƙara yin haske. Domin ba duk abin da yake da amfani a wani yanayi na likitanci ne yake nufin kowa zai iya amfani da shi yadda ya ga dama ba.
