Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai bai wa Gwamnan Katsina shawara kan harkokin jam’iyyu, Alhaji Shafiu Abdu Duwan, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa, bisa amincewa da sake gina hanyar Bindawa zuwa Dallaje, Doro, Giremawa da Duwan Junction.
Alhaji Duwan ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa rayuwar al’ummar yankin.
Gwamna Raɗɗa ya amince da bayar da aikin sake gina hanyar a yayin taron Majalisar Zartarwar karo na 16 da ya gudana a gidan gwamnatin Katsina.
Bayan kammala aikin hanyar zai taka muhimmiyar rawa wajen haɗa al’ummomi da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da safarar kayayyaki.
” Haka kuma zai sauƙaƙa wa manoma da ’yan kasuwa kai kayayyaki zuwa kasuwanni, tare da buɗe ƙarin damarmaki na harkokin kasuwanci da sauran ayyukan tattalin arziki a yankin,”Duwan yace.
Haka kuma, aikin zai inganta hanyar zuwa makarantu, asibitoci da sauran muhimman wuraren hidima, tare da rage matsalolin sufuri da al’ummar yankin ke fuskanta.
Mai ba gwamna shawarar ya buƙaci al’ummar yankin da su ci gaba da mara wa gwamnatin jihar Katsina baya tare da goyon bayan ayyukan raya ƙasa da take aiwatarwa, yana mai cewa haɗin kan al’umma zai taimaka wajen samun karin ci gaba da bunƙasa yankin.
