Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta amincewa da tallafin gaggawa ga ma’aikata a faɗin ƙasar, ta hanyar ƙarin alawus na albashi, domin rage tasirin hauhawar farashin man fetur.
Kungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta samar da ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida da kuɗin Naira, domin rage matsin lambar da hauhawar farashin man fetur ke haifarwa ga al’umma.
NLC ta kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙarfin ajiyar man fetur na ƙasa, domin shawo kan matsalolin gaggawar makamashi da kuma ƙarfafa tsaron makamashi.
A wata sanarwa da Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya fitar a ranar Laraba, ya yi gargaɗin cewa ƙarin farashin fetur zai ƙara tsananta halin matsin tattalin arzikin da ’yan Nijeriya ke fuskanta.
Bincike ya nuna cewa a halin yanzu ana sayar da litar fetur kan kusan Naira 1,430 a manyan biranen ƙasar, yayin da farashin ke ƙara tashi a wuraren da ba su da sauƙin samun man.
A cikin sanarwar mai taken “A Ceto Halin Da Ake Ciki Yanzu”, Ajaero ya tambayi dalilin da zai sa gwamnati da ke neman sake komawa mulki cikin watanni masu zuwa ta tsaya tana kallon ’yan kasuwar man fetur suna ƙara jefa ’yan ƙasa cikin wahala da sunan cire tsarin tallafin man fetur. NLC ta ce babu laifi gwamnati ta tallafa wa buƙatun ’yan ƙasa, musamman a irin wannan yanayi na gaggawa da ake ciki.
Ajaero ya bayyana cewa duk lokacin da farashin sufuri ya tashi, hakan kan haifar da ƙarin farashin kayan abinci, haya, kuɗin makaranta da sauran muhimman kayayyaki da hidimomi a faɗin ƙasar.
Ya ce ƙarin farashin da aka samu a yanzu ya zo ne a lokacin da matsin da gwamnati ke yi wa ’yan kasuwar man fetur domin rage farashin famfunan mai, bisa la’akari da saukar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, ya fara haifar da sakamako.
Sanarwar ta ce, ƙungiyar na matuƙar damuwa da hauhawar farashin litar fetur a faɗin ƙasar. A manyan biranen da ake samun fetur cikin sauƙi, farashin ya kai Naira 1,430, yayin da yake ƙara tsada a wuraren da samun man ke da wahala.
NLC ta ce, wannan yanayi ya jefa albashi da kuma rayuwar al’umma cikin matsananciyar barazana, tare da ƙara zurfafa talauci da kuma rage ingancin rayuwa.
ƙungiyar ta ce, ƙarin kuɗin sufuri kan shafi kusan komai, ciki har da kuɗin makaranta, haya, kuɗaɗen hidimomi da kayan abinci.
A cewar Ajaero, wannan sabon tashin farashin ya zo ne a daidai lokacin da matsin da gwamnati ke yi wa ’yan kasuwar man fetur domin farashin ya yi daidai da na ɗanyen mai a kasuwar duniya ya fara haifar da sakamako.
Ya ce, duk da cewa tashin farashin ya samo asali ne daga sake ɓarkewar rikici a yankin Gulf, halin da ake ciki a Nijeriya bai kamata ya kai wannan matsanancin mataki ba.
Ajaero ya ce kasancewar Nijeriya ƙasa mai arzikin ɗanyen mai, tare da samun ƙarfin tace mai a cikin gida, ko da yake mafi yawansa na hannun kamfanoni masu zaman kansu ne, ya kamata ya ba ƙasar wata dama ta kare al’ummarta daga tasirin rikice-rikicen kasuwar mai ta duniya.
Ya ƙara da cewa Nijeriya, a matsayinta na ƙasa mai ɗumbin albarkatun mai da iskar gas, ta cancanci samun wani matakin kariya daga illolin rikice-rikicen yankin Gulf da sauran matsalolin da ke tasiri ga kasuwar mai.
ƙungiyar NLC ta kuma yi kira da a ƙara ɗaukar matakan gwamnati domin magance matsalar rashin tsaro da ta ƙara ƙamari a sassan Nijeriya a baya-bayan nan.
Shugaban NLC ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan da za su kare iyalai da ’yan kasuwa daga illar ƙarin farashin man fetur.
Ajaero ya ce matakan ya kamata su kasance wani ɓangare na faɗaɗɗen shirin samar da kariya ga ’yan Nijeriya daga tasirin hauhawar farashin kayayyakin man fetur.
Ya ce, gwamnati ta kamata ta gaggauta samar da ƙarin alawus mai ma’ana ga ma’aikata, ta sayar da isasshen ɗanyen mai ga matatun cikin gida da kuɗin Naira, tare da ƙara ƙarfin ajiyar man fetur na ƙasa domin tunkarar matsalolin gaggawar makamashi da ƙarfafa tsaron makamashi.
A cewarsa, waɗannan matakai za su taimaka wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa darajar tattalin arziki, tare da taimakawa wajen tunkarar sauye-sauyen ƙalubalen tsaro.
Ya jaddada cewa babu laifi gwamnati ta tallafa wa buƙatun ’yan ƙasa, musamman a irin wannan yanayi na gaggawa.
Ajaero ya ce, a halin yanzu babu wata ƙasa mai arzikin mai da ƙungiyar ta sani da ba ta ɗauki wani mataki na tallafa wa jama’arta ko samar da wasu matakan rage raɗaɗin matsin tattalin arziki a irin wannan lokaci mai wahala ba.
Ya ce buƙatar ɗaukar waɗannan matakai na ƙara zama cikin gaggawa saboda gwamnati na samun ƙarin kuɗaɗen shiga a kasuwar ɗanyen mai ta duniya, inda farashin yake tsakanin dala 35 zuwa dala 40 kan kowace ganga sama da adadin da aka yi hasashe a kasafin kuɗin gwamnati.
A cewarsa, wannan ƙarin kuɗin na iya kai wa tiriliyanin Naira a kowane wata, wanda ya kamata gwamnati ta ɗauke shi a matsayin ƙarin kuɗin shiga da ya samu ba zato, tare da amfani da shi wajen rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin tsadar rayuwa.
