Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Johannesburg, Babban Birnin ƙasar Afirka ta Kudu, ya fitar da gargadin tsaro ga ’yan Nijeriya da ke zaune a yankunan Kempton Park, Rhodesfield da sauran wuraren da ke kusa da Ekurhuleni, sakamakon mutuwar mata takwas da rundunar ’yan sandan Afirka ta Kudu (SAPS) ke gudanar da bincike a kan al’amuran.
A cikin sanarwar tsaron da ofishin ya fitar ranar 16 ga Satumba, 2026, ya ce mutuwar matan ta faru ne cikin kimanin watanni biyu, lamarin da ya sa aka tura wata tawagar bincike mai ƙunshe da jami’an hukumomin tsaro daban-daban da kuma ƙwararrun jami’an bincike.
“Ofishin Jakadancin Tarayyar Nijeriya da ke Johannesburg na son jawo hankalin ’yan Nijeriya cikin gaggawa kan matsalolin tsaro masu tsanani da ke tasowa, bayan mutuwar mata takwas waɗanda rundunar ’yan sandan Afirka ta Kudu (SAPS) ke gudanar da bincike a kansu a cikin Ekurhuleni da kewayenta, gabashin Johannesburg.
“Mutuwar ta faru cikin kimanin watanni biyu, kuma hakan ya sa aka tura wata tawagar bincike mai ɗauke da ƙwararrun jami’an tsaro da hukumomin bincike,” in ji sanarwar.
Ofishin ya ce masu binciken sun gano “wasu abubuwa masu tayar da hankali da suka yi kama da juna” a wasu daga cikin al’amuran, kuma suna binciken ko akwai wata alaƙa tsakanin abubuwan da suka faru da kuma irin girman wannan alaƙa.
Sai dai ofishin ya jaddada cewa har yanzu SAPS ba ta tabbatar da cewa mutum guda ne ya aikata kashe-kashen ba, kuma ba ta tabbatar da cewa akwai wani mai kashe mutane da yawa a jere, wato serial killer, da ke da hannu a lamarin ba.
Ofishin ya ce har yanzu ana ci gaba da binciken yanayin mutuwar kowace daga cikin matan, amma ya bayyana cewa lamarin ya isa ya sa ’yan Nijeriya, musamman mata da ’yan mata da ke zaune, aiki, karatu, motsa jiki, gudanar da harkokin zamantakewa ko kuma yawan bi ta yankunan da abin ya shafa, su ƙara yin taka-tsantsan tare da ɗaukar matakan kare kansu.
Ya ce damuwar ofishin ba ta samo asali daga jerin abubuwan da suka faru kwanan nan kaɗai ba, har ma da yanayin yawaitar aikata laifuka a lardin Gauteng.
A cewar sanarwar, ƙididdigar laifukan da SAPS ta fitar na baya-bayan nan ta nuna cewa an samu kashe-kashe 1,223 da laifukan lalata 2,369 a Gauteng tsakanin watan Janairu da Maris na 2026. A cikin wannan lokaci kuma, SAPS ta samu rahoton laifukan taɓa mutane ko aikata laifi da suka shafi mutane guda 39,094 a lardin.
Sai dai ofishin ya lura cewa waɗannan ƙididdigar ba sa tabbatar da wata alaƙa tsakanin mutuwar matan takwas da wani takamaiman salon aikata laifi.
Ofishin Jakadancin ya shawarci ’yan Nijeriya, musamman mata, da su guji yin tafiya da ƙafa, guje-guje ko motsa jiki su kaɗai a wuraren da ba kowa, wuraren da ba su da isasshen haske, hanyoyin da ba a cika amfani da su ba ko kuma wuraren da ba su saba da su ba, ciki har da fili da hanyoyin da ke keɓe.
Haka kuma, ya bukaci ’yan Nijeriya su riƙa yin motsa jiki da kuma tafiye-tafiye tare da wasu mutane idan hakan zai yiwu, su riƙa sauya hanyoyin da suke bi da kuma lokutan da suke fita motsa jiki, tare da guje wa yawan amfani da wurare masu kaɗaici.
Ofishin ya kuma shawarci mazauna yankunan da su kasance cikin lura da abubuwan da ke faruwa a kewayensu, tare da guje wa ɗaukar dogon lokaci suna amfani da belun kunne ko wayar hannu yayin tafiya ko motsa jiki a wuraren da ba a iya gani sosai ko kuma wuraren da ba a cika samun masu tafiya da ƙafa ba.
Ya ƙara da cewa ya kamata ’yan Nijeriya su riƙa sanar da ’yan uwansu, abokansu ko wasu amintattun mutane inda suke shirin zuwa, hanyar da za su bi da kuma lokacin da suke sa ran dawowa.
Ofishin ya kuma yi gargadin kada ’yan Nijeriya su riƙa yaɗa hotuna, sunaye, bidiyo, saƙonnin murya ko zarge-zargen da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, musamman waɗanda ke ƙoƙarin bayyana wasu mutane a matsayin waɗanda ake zargi da aikata laifukan.
Ya ce irin wannan yaɗa bayanai na iya kawo cikas ga binciken da ake gudanarwa, jefa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba cikin matsala, tare da kawo cikas ga ayyukan hukumomin tsaro.
Ofishin Jakadancin ya bayyana cewa gargadin ba na nufin ya haifar da tsoro ko hana ’yan Nijeriya zirga-zirgar da doka ta ba su damar yi ba, sai dai manufarsa ita ce tabbatar da cewa al’umma ta samu bayanan da suka dace domin ɗaukar matakan kariya masu ma’ana yayin da ake ci gaba da bincike.
Ya kuma jaddada cewa bai kamata a ɗauki matakan kariyar da aka bayar a matsayin ɗora wa mata nauyin kare kansu daga tashin hankali ba, ko kuma a matsayin madadin ingantaccen aikin ’yan sanda, bincike da kuma tabbatar da an hukunta masu laifi.
Ofishin ya ce matakan da ya bayar “matakan kariya ne na zahiri waɗanda za su iya rage fuskantar haɗarin gaggawa, yayin da hukumomin tsaro ke gudanar da bincike kan yanayin mutuwar matan.”
Ofishin Jakadancin ya jajanta wa iyalai da ’yan uwan matan da suka rasu, tare da roƙon duk wanda yake da sahihin bayani da zai taimaka wajen binciken da ya miƙa bayanin kai tsaye ga SAPS, maimakon ya yaɗa shi a kafafen sada zumunta.
Ya ce zai ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke faruwa tare da tuntuɓar Babban Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Pretoria da kuma hukumomin Afirka ta Kudu da abin ya shafa.
Sanarwar ta bayyana cewa lambar gaggawa ta SAPS ita ce 10111, yayin da Crime Stop ke karɓar bayanan sirri ba tare da bayyana sunan mai bayarwa ba ta lamba 08600 10111. Haka kuma ana iya kiran lambar gaggawa ta wayar hannu 112.
’Yan Nijeriya za su iya amfani da manhajar MySAPS wajen miƙa bayanan da za su iya taimakawa wajen bincike.
