2027: ’Yan majalisa 100 sun rasa tikiti, mata 123 na takara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUH’D da SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kusan ’yan Majalisar Wakilai 100 ne daga cikin waɗanda ke kan kujerunsu a yanzu ba za su sake komawa majalisar a shekarar 2027 ba, bayan sun kasa samun tikitin jam’iyyunsu na sake tsayawa takara ko kuma suka zaɓi neman wasu manyan kujerun zaɓe.

Wani bincike da aka gudanar bisa jihohi ya nuna cewa ’yan Majalisar Wakilai 262 daga cikin waɗanda ke kan kujera a yanzu sun samu damar sake tsayawa takara, ko dai a ƙarƙashin jam’iyyunsu na yanzu ko kuma bayan sauya sheƙa zuwa wasu jam’iyyu.

Daga cikin manyan jami’an majalisar da ba za su dawo ba akwai Shugaban Masu Rinjaye, Julius Ihonvbere, na jam’iyyar APC daga Edo; Mataimakin Bulaliyar Masu Rinjaye, Isiaka Ayokunle Isiaka, na APC daga Ogun; Shugaban ’Yan Adawa, Fred Agbedi, na PDP daga Bayelsa; Mataimakin Bulaliyar ’Yan Adawa, Manu Soro, na PDP daga Bauchi; Mataimakin Shugaban ’Yan Adawa, Abdulsamad Dasuki, na ADC daga Sokoto; da kuma Mataimakin Bulaliyar ’Yan Adawa, George Ozodinobi, na NDC daga Anambra.

Daga cikin manyan jami’an Majalisar, Shugaban Bulaliyar Majalisar, Usman Bello Kumo, da Mataimakin Shugaban Majalisar, Abdullahi Ali, su ne kaɗai suka samu tikitin sake tsayawa takara. Manu Soro da Abdulsamad Dasuki dai sun zaɓi ba za su sake neman kujerunsu ba, don haka ba su shiga zaɓen fidda-gwanin jam’iyyunsu ba.

Jihar Kano ce ta fi yawan ’yan Majalisar da suka samu tikitin dawowa, inda 23 daga cikin ’yan Majalisar 24 na jihar suka samu damar sake tsayawa takara. Legas ta biyo baya da ’yan majalisa 15 daga cikin 24 da suka samu tikitin dawowa, yayin da Kaduna ke da ’yan majalisa 15 da za su dawo daga cikin 16 da jihar ke da su a majalisar.

Haka kuma, bayanai sun nuna cewa mafi yawan ’yan majalisar da suka sauya sheƙa daga jam’iyyunsu na baya, musamman a Kano da Ribas, sun samu tikitin sake tsayawa takara a ƙarƙashin sabbin jam’iyyun da suka koma.

A gefe guda kuma, Jam’iyyar PDP ta tsayar da kusan mata 21 takarar kujerun Majalisar Wakilai, yayin da ta tsayar da ’yan takarar mata shida domin kujerun Majalisar Dattawa a faɗin ƙasar.

Daga cikin mata da PDP ta tsayar wa takarar Majalisar Wakilai akwai Umoh Esther Robson daga Ikot Abasi/Mkpat Enin/Eastern Obolo a Akwa Ibom; Okeke Chidinma Ngozi daga Onitsha North/Onitsha South a Anambra; Okoli Ogochukwu Evangeline daga Aguata; Okafor Jenifer daga Oyi/Ayamelum; Onuora Helen Uju daga Njikoka/Dunukofia/Anaocha; Chita Chiamaka Modester daga Idemili North/Idemili South; da Garba Maryam Bagel daga Bogoro/Dass/Tafawa Balewa a Bauchi.

Sauran ’yan takarar matan PDP sun haɗa da Edom Peace Eyo daga Calabar South/Akpabuyo/Bakassi a Cross River; Blessing Chinazam daga Abakaliki/Izzi a Ebonyi; Jemitola Elizabeth daga Akoko-Edo a Edo; Nwadike Peace Adanma daga Isu/Njaba/Nkwerre/Nwangele a Imo; Iheme Ndidi Olachi Ulumna daga Owerri Municipal/Owerri North/Owerri West; Isiyaku Suwaiba daga Ngaski/Shanga/Yauri a Kebbi; da Omoshola Gbemisola Holymary daga Ibeju-Lekki a Legas.

Haka kuma, PDP ta tsayar da Akinsanya Idowu Bimpe daga Shomolu a Lagos; Aliyu Biriskillia Beauty daga Akwanga/Nassarawa Eggon/Wamba a Nasarawa; Musa Hauwa daga Bosso/Paikoro a Niger; Okuboyejo Rasheedat Temitope daga Ado-Odo/Ota a Ogun; Alao Elizabeth Folashade daga Ibarapa East/Ido a Oyo; da Ewo Prescilia Richard daga Abua/Odual/Ahoada East a Rivers.

A takarar Majalisar Dattawa kuwa, PDP ta tsayar da Oliata Chinenye Edith a Anambra ta Arewa; Ortom Eunice Edith a Benue ta Arewa; Nwachi Maria Ude a Ebonyi ta Kudu; Fatuyi Olajuyigbe Monica Adesola a Ekiti ta Tsakiya; Ayenioye Olabisi a Ekiti ta Kudu; Natasha Akpoti Uduaghan a Kogi ta Tsakiya; da Iyabo Obasanjo a Ogun ta Tsakiya.

Sauran jam’iyyun da suka gabatar da ’yan takara domin kujerun Majalisar Wakilai sun haɗa da NNPP mai ’yan takara takwas, ADP 30, NRM 20, PRP ɗaya, ZLP 17, SDP 34, APP 15, AA 10, Accord 14, DLA 12, LP 20, APGA biyar, APM 40, NDP 12, AAC tara, BP ɗaya da YPP huɗu.

A Majalisar Dattawa kuma, jam’iyyun da ke fafatawa sun haɗa da ZLP da ’yan takara takwas, APP biyar, ADP 11, AAC huɗu, DLA shida, Accord 11, APGA uku, NNPP huɗu, NRM tara, APM 12, LP takwas, YPP shida, NDP uku, SDP bakwai, AA shida da YP ɗaya.

Rahoton ya kuma bayyana cewa ɗan takara guda mai matsalar gani da kuma wani ɗan takara zabiya, su ma na cikin waɗanda ke fafatawa a zaɓen Majalisar Wakilai na 2027.

A wani ci gaban kuma, aƙalla mata guda 123 ne za su fafata, domin neman kujerun Majalisar Dattawa guda 109 a zaɓen shekarar 2027, yayin da jimillar ’yan takarar da suke neman kujerun majalisar ta ƙasa ta ƙoli ta kai 1,303.

Daga cikin ’yan takarar 1,303, mata 123 ne, yayin da maza suka kai 1,180, kamar yadda bayanan jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar suka nuna.

Daga Jihar Abia akwai Umunnah Favour Ugochi (APM), Nkechi Nwaogu (NDC), Ihekandu Gladys Chioma (ZLP) da Nwosu Eucharia (APP), yayin da daga Adamawa akwai Bagardi Charity (ADP). A Akwa Ibom kuwa akwai Ukpong Mary Iniobong (AAC), Ibokette Princess Victoria (DLA), Inyang Peace Martins (A), Udoudo Comfort Etim (AA), Akpan Unyime Mbono (AAC), Akpabio Patience Christopher Ibanga (ADC), Itongeshiet Amaiso Solomon (BP), Priscilla Akpanumo (ADP), Ekanem Joy Victor (AAC) da Ufot Patricia Gabriel (ZLP).

A Anambra akwai Oduah Stella Adaeze (APGA), Olieh Ndidi Christiana (NRM), Oliata Chinenye Edith (PDP), Ekwunife Uche Lilian (APC), Mbakwe Helen I. (ZLP) da Benson-Oraelosi Chibuogwu Maryanne (APC), yayin da Bauchi ke da Mohammed Safiya Illiasu (NNPP) da Shehu Hannatu (ADP). A Bayelsa kuwa akwai Oruama Peace (APM), George Ruth (DLA), Iwokura Beauty (ZLP), Douglas Preye (A), Zuonaki Ebiere Esther (LP) da Mohammed Tombra (YPP).

Daga Benue akwai Achineku Vester Suur (ADP), Ortom Eunice Erdoo (PDP) da Odeh Uleko Hannah (NDP), yayin da Borno ke da Baba Gana Zannah (ADC). A Cross River akwai Amoikwen Godwin (LP), Ake Abuashe Grace (SDP), Mbeh Ifumi Ofere (YPP), Inyang Florence (PDP) da Edet Helen Ekanem (YPP).

A Delta akwai Dema Onome Bernice (LP), Omoraka Amanda (YPP), Nwabuokei Vivian Ify (A), Nwankwo Maryann Oluebube (APM) da Avwivoerjore Esther (ZLP), yayin da Ebonyi ke da Nwachi Maria Ude (PDP). A Edo kuwa akwai Okonofua Herberta Inemezele (ADC), Adudu Evelyn Omonigho (APM), Oisamoje Maria Evuarherhe (NDC), Ekhorutomwen Osahenoma (ADP) da Epelle-Asemota Bridgitte Osayuki (NDC).

A Ekiti akwai Fatuyi-Olajuyigbe Monica Adesola (PDP) da Ayenioye Olabisi (PDP), yayin da Enugu ke da Nwekeke Chinasa Annastesia (A), Ujam Cynthia Onyinye (APP), Aguocha Adaku Anna (NDC), Agu Philomina (A), Ani Juliet Nkechi (ADC) da Ugwuogo Nkechi Jacinta (APM). A Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) kuma akwai Omotosho Rashida Ololade (AA), Ireti Heebah Kingibe (ADC), Austenpeters-Pam Iyabode Amanda (NDC) da Benyeogor Blessing Ufedojo (YPP).

Daga Gombe akwai Hamma Tabitha (APM), Abdussalam Sarah (NRM) da Salisu Khadija Yahaya (ZLP), yayin da Imo ke da Ibe Chinazom Ibezue (A), Okafor Loveth (AA), Uzoma Betty Ijeuru (APGA), Igwe Ebere Stella (A) da Ibekwe Nkiru (ADC). A Kaduna akwai Jenifer Agbaje (YPP), Badamasi Hafsat (ADP) da Laura Yimi Lucas (SDP), yayin da Kano ke da Aliyu Rabi (AAC) da Muhammed Jamila (NDP).

A Katsina akwai Al Samaila Amajir (SDP) da Amina Lawal Rafindadi (APM), yayin da Kebbi ke da Kabir Fatima (APM). A Kogi kuwa akwai Suzan Jagbadi (A), Akpoti-Uduaghan Natasha Hadiza (PDP), Patient Ogbadu Gold (A), Ocheja Berikisu (DLA) da Olorunmagba Ekene (NRM).

Daga Kwara akwai Temako Naomi (ADP), Ibrahim Ramat (APP), Owolabi Felicia (APM), Adesola Kehinde (AA), Abdulahi Risikat Motunrayo (ADC), Abdulkarim-Adisa Maryam Ayoola-Fadekemi (LP) da Anifowoshe Grace (SDP). A Lagos akwai Maduka-Sunday Blessing Maria (A), Adebule Idiat Oluranti (APC) da Adebowale Princess Teniola Anike (NNPP).

A Ogun kuwa akwai Sado Evelyn Mayowa (BP), Awosusi Racheal (NRM), Obasanjo Iyabo (PDP) da Itakpe Oluwayemisi Abiola (APM), yayin da Ondo ke da Omolabaro Shina Omotilewa (NRM). A Osun akwai Adeniyi Yemisi (ADP), Becky Foluso James (DLA), Oguntade Sabainah Adebola (NRM), Onile Elizabeth Ifepade (ZLP), Oni Oluwatoyin Esther (NRM), Rufai Mariam Adeola (AA) da Adesina Bola Dorcas (LP).

A Oyo akwai Adediji-Ogunsanya Funmilayo Ayonade (NDP), Ogunesan Hannah Olawumi (APC), Ojekunle Abigail Olanike (NDC) da Oloyede Esther (ADP), yayin da Plateau ke da Luka Sekyen Lekshak (YPP), Rose Bitrus Mwanti (ADC) da Inah Deborah Ajang (NRM).

Daga Ribas akwai Wokekoro Beauty Dike Chinonso (APP), Itubo Beatrice (LP), Lessi Naasi Susan (SDP), Ololube Charity Chizhim (AA), Abusi Tammy C (ADP), Opoli Aneni Inyamoyio (DLA) da Sokari George Georgina (NNPP). A Sokoto kuma akwai Abdulrahman Halima (APM), yayin da Taraba ke da Afiniki Yarima (APGA) da Yubuin Victoria Samuel (LP).

A Jihar Zamfara kuwa akwai Muhammad Fatima (ZLP) da Sipawa Aisha (ADP).

Daga cikin fitattun ’yan takarar da ke cikin wannan jerin akwai Natasha Akpoti-Uduaghan da ke neman kujerar Kogi Central a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Ireti Kingibe daga Babban Birnin Tarayya Abuja a ƙarƙashin ADC, Nkechi Nwaogu daga Abia Central a ƙarƙashin NDC, da Idiat Oluranti Adebule daga Lagos West a ƙarƙashin APC.

Yawan mata 123 da ke neman kujerun Majalisar Dattawa a zaɓen 2027 na nuna ƙarin shigar mata cikin takarar manyan mukaman siyasa, yayin da zaɓen ke ƙara kusantowa.

By ukarofi

Leave a Reply