
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mutane da dama sun rasu a lokacin da wani sashi na wajen haƙar ma’adinai a ƙauyen Mayo Kam ya rufta a Ƙaramar Hukumar Bali da ke Jihar Taraba a ranar Alhamis.
Al’amarin ya faru ne da rana a lokacin da masu haƙar suke aiki a gurin, lamarin da ya yi sanadiyyar masu yawa daga cikinsu sun rasa rayukansu. A yayin haɗa wannan rahoto ba a san ainihin adadin waɗanda suka rasu ba. Saidai ana hasashen akwai yiwuwar adadinsu ya kai mutum 20.
Da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Juma’a, Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba, Victor Mshelizah ya ce zuwa yanzu dai an tabbatar da rasuwar mutane biyar yayin da ake ƙoƙarin ceto waɗanda iftila’in ya shafa.
Ya ce, gurin haramtacce ne a ƙauyen Mayo Kam da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bali, inda tun a jiya Alhamis suka aike da jami’ai zuwa wajen. Wannan al’amari ya jefa mazauna yankin cikin jimami yayin da dama daga cikin waɗanda hakan ya shafa ‘yan ƙauyen ne.
Hakan na zuwa ne kwana guda da aka samu labarin rasuwar masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba guda 37 a ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) da ke Jihar Neja, inda daga bisani Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kwamandan NSCDC na jihar tare da bayar da umarnin bincike.
