Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda ya ɗora wa Bankin Zenith da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya alhakin biyan diyyar Naira miliyan 85 saboda rufe asusun wani abokin ciniki ba bisa ƙa’ida ba, bisa wani umarnin kotu da bai da inganci.
A wani hukunci da kwamitin alƙalai uku na Kotun ɗaukaka ƙara ya yanke baki ɗaya ranar Litinin, kwamitin da Mai Shari’a Adebukola Banjoko ta jagoranta ya yi watsi da ƙarar da Bankin Zenith ya shigar, yana mai cewa ba ta da hujjar da za ta sa a karɓe ta.
Hakan ya tabbatar da hukuncin da Mai Shari’a S.U. Bature na Babbar Kotun Abuja ya yanke ranar 16 ga Yuli, 2025, inda ya bayar da umarnin biyan Naira miliyan 60 a matsayin diyya da kuma Naira miliyan 25 a matsayin kuɗin shari’a, a kan Bankin Zenith da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya tare.
Shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar da Paulyn Abhulimen ta shigar a madadin kamfanin lauyoyinta, Abhulimen & Co, bayan da Bankin Zenith ya daskarar da asusun kamfanin a shekarar 2024.
Abhulimen ta shaida wa kotun cewa ta gano an takaita amfani da asusun ne bayan ta kasa shiga cikinsa ko yin wata mu’amala da kuɗin da ke ciki.
A cewarta, daga baya wani jami’in bankin mai suna Obi Okafor ya sanar da ita cewa bankin ya sanya wa asusun dokar “Post No Debit” (PND), wato dakatar da fitar da kuɗi daga asusun, tun ranar 13 ga Maris, 2024.
An ce bankin ya ɗauki wannan mataki ne bisa wani umarnin wucin-gadi da aka samu ba tare da sanar da ɗayan ɓangaren ba (eɗ parte order), wanda Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta samo daga Kotun Alƙalin Majistare da ke Mararaba Gurku a Jihar Nasarawa.
An shigar da ƙarar a ƙarƙashin lambar FCT/HC/CV/2194/2024, inda aka sanya Bankin Zenith da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya a matsayin waɗanda ake ƙara.
A hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar, Mai Shari’a Bature ya bayyana cewa Kotun Alkalin Majistare da ke Mararaba Gurku ba ta da ikon shari’a, ta fuskar yankin da kuma nau’in shari’ar, na bayar da umarnin daskarar da asusun bankin. Mai shari’ar ya ce ba a fahimci dalilin neman irin wannan umarni a gaban kotun majistare da ke ƙarƙashin ikon shari’ar Jihar Nasarawa ba. Ya ƙara da cewa, kotun majistaren ba ta da hurumin yanki na sauraron buƙatar rufe asusun.
A cewar hukuncin, kotunan majistare ba su da hurumin sauraron buƙatar neman umarnin rufe asusun bankin mutum, don haka bai kamata a gabatar da irin wannan buƙata a gabanta ba tun farko.
Kotun ta kuma ce sashen shari’a na Bankin Zenith, wanda ya ƙunshi ƙwararrun lauyoyi, ya kamata ya san wannan matsayi na doka kuma ya ɗauki matakin da ya dace, maimakon bin umarnin kotun da ba ta da hurumin bayar da shi.
Saboda haka, Mai Shari’a Bature ya bayyana cewa Bankin Zenith ya yi kuskure wajen sanya dokar PND a kan asusun Abhulimen & Co bisa umarnin wata kotu da ba ta da hurumin yin hakan.
Bugu da ƙari, kotun ta gano cewa bankin ya yi sakaci saboda bai sanar da abokin cinikinsa cewa an rufe asusunsa ba. Mai Shari’a Bature ya ce bankin yana da nauyin kula da muradun abokin cinikinsa, ciki har da sanar da ita cewa an sanya takunkumi kan asusunta.
Ya ce, rashin sanar da mai asusun halin da ake ciki ya zama sakaci daga ɓangaren bankin, tare da karya nauyin kulawa da bin ƙa’idojin da ya rataya a kansa.
Kotun ta kuma bayyana cewa umarnin wucin-gadi na daskarar da asusun banki da aka bayar ba tare da sanar da ɗayan ɓangaren ba, ba zai ci gaba da aiki har abada ba tare da bin ƙa’idojin doka ba.
Saboda haka, ta umarci Bankin Zenith da gaggauta cire dokar PND da aka sanya wa asusun Abhulimen & Co. Haka kuma, Mai Shari’a Bature ya umarci bankin da ya wallafa cikakkiyar neman gafara ga mai ƙara a cikin manyan jaridun ƙasa guda biyu, tare da sanya saƙon neman gafarar a shafin yanar gizon bankin.
Da wannan hukunci na Kotun ɗaukaka ƙara, an tabbatar da dukkan umarnin da Babbar Kotun Abuja ta bayar, ciki har da biyan Naira miliyan 60 a matsayin diyya da Naira miliyan 25 a matsayin kuɗin shari’a da aka ɗora wa Bankin Zenith da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya.
