
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An tura sabon Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Sibil Difens (NSCDC), mai suna Abdulhamid Salisu Kabara domin jagorantar rundunar reshen Jihar Neja.
Hakan ya biyo bayan dakatar da Suberu Siyaka Aniviye ne a muƙamin sakamakon mutuwar matasa masu aikin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba su 37 a ofishin hukumar..
A sanarwar da jami’in hulɗa da jama’ar NSCDC, DSC Abubakar Rabi’u Muti ya fitar, ya ce Kabara ya maye gurbin Aniviye ne a matsayin, wanda halin yanzu an dakatar da shi bisa hannu a mutuwar matasan.
Muti ya bayyana cewa, Kabara ya kama aiki ne a daidai lokacin da matasan da aka kama bisa zargin aikin haƙar ma’adinai ba bisa doka ba a jihar suka rasu a ofishin NSCDC bayan tsare su na tsawon sama da sa’o’i 24.
Jami’in ya bayyana jimami bisa abin alhinin tare da aike wa iyalan waɗanda suka rasu saƙon ta’aziyyarsu da dukkan wanda abin ya shafa.
Ya kuma jaddada aniyar hukumar ta gudanar da bincike tare da tabbatar da gurfanar da dukkan masu hannu a ciki, yana mai wajibi ne a bai wa rayukan al’umma kariya yayin ƙoƙarin tabbatar da biyayya ga doka.
