Uku sun rasu yayin da 5 suka jikkata a sabon harin kasuwar Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mutane uku aka halaka da raunata wasu biyar bayan wasu ‘yan bindiga sun buɗe wa jama’a wuta a kasuwar ‘Yan Gwari da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a Jihar Filato.

Al’amarin, wanda ya auku a ranar Juma’a, ya haifar da fargaba kan halin tsaro a Mangu da wasu sassan Jihar Filato, inda aka samu munanan hare-hare a makonnin da suka gabata.

Waɗanda suka rasu a harin sune Nanker Andrew, Delshak Jacob da kuma Jessica Thomas. Sun rasa rayukansu ne a wajen da al’amarin ya faru. Sai kuma Polina Colis, Gloria Fwanshak, Sekyen Lonkat da Bamrat Thomas, waɗanda suka jikkata kuma suke karɓar magani a halin yanzu.

A cewar shaidu, maharan sun afka wa jama’a ne yayin da ake tsaka da hada-hada a kasuwar, inda suka riƙa harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa ‘yan kasuwar da kwastomomi da wasu mazauna tserewa zuwa bayan gari domin neman mafaka.

Wannan al’amari ya tayar da hankalin jama’a musamman ganin yadda jama’a suka watse ba tare da wani shiri ba yayin da su ma maharan suka fice daga yankin. Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata, an kai wasu wuraren karɓar magani a yankin yayin da aka garzaya da wasu kuma zuwa Jos domin ba su kulawar asibiti.

Wannan hari na zuwa ne kwanaki kaɗan da Jihar Filato ta fuskanci wasu hare-hare a ƙauyuka da dama musamman a ƙananan hukumomin Mangu, Jos ta Kudu, Riyom da Barikin Ladi. Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wani bayani kan al’amarin ba.

By Babaji

Leave a Reply