
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da Hussain Yusuf Datti na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin mazaɓar Dawakin Kudu ta Jihar Kano.
Bature zaɓen, Farfesa Ibrahim Tajo-Suraj ne ya bayyana haka a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu. Ya ce, Yuzuf Datti ya yi nasarar ne sakamakon samun ƙuri’a 22,890, wanda ya ba shi damar doke Habib Hamisu na Peoples Redemption Party (PRP) da ya samu ƙuri’a 270.
Haka kuma, ya ce Abdullahi Adamu na Peoples Democratic Party (PDP), ya samu ƙuri’a 108, yayin da Bala Mohammed-Sani na Action Democratic Party (ADP) ya samun 89. Aliyu Abdullahi na All Peoples Party (APP) ya samu ƙuri’a 53, sai Abubakar Yahya-Mohammed na Labour Party mai guda 39.
Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana duk da cewa jama’a sun yi tururuwa wajen fitowa domin kaɗa ƙuri’arsu. Saidai, ba a samu hamayya mai ƙarfi ba kasancewar jam’iyyun NDC da ADC ba su shiga zaɓen ba.
An gudanar da wannan zaɓe ne sakamakon wanda ke kan kujerar ya lashe wani zaɓen cike gurbi na kujerar ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa da aka gudanar a kwanakin baya.
