Mun shirya tunkarar zaɓen 2027 – Mansur Gulma

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban yaƙin neman zaɓen karamar hukumar Argungu a ƙarƙashin jam’iyyar ADC Alhaji Mansur Adamu Gulma ya bayyana cewa sun shirya tsaf don tinkarar zaɓe mai zuwa na shekarar 2027.

Ya yi wannan bayanin ne a wani taron matasa da aka gudanar a garin Argungu ƙarshen makon da ya gabata. Alhaji Mansur ya ce a fagen siyasa yanzu ba wanda zai sake yaudarar matasa in sha Allahu saboda a baya ana yaudarar mutane musamman matasa da sunan za a taimaka masu wajen samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar su, kuma daga baya a mayar da su yan jiran gawon shanu. Wannan lokacin ya wuce, saboda haka yanzu al’umma sun gane yaudarar su kawai a ke yi.

Ba zage-zage ba cin zarafin kowa amma dai duk wanda ke ganin zai iya to a haɗu ranar zaɓe ya sha mamaki.

Ya ja kunnen matasa da ke goyon bayan sa da cewa su cigaba da biyayya ga dokokin ƙasa da na jam’iyya kamar yadda aka faro daga farko wanda yin haka wani mataki ne na nasara.
“Za mu cigaba da wayar da kawunan mutane birni da ƙauyuka har sai yadda hali ya yi.” Inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply