Gwamnatin Zamfara ta amince da ƙarin kaso 95 na albashin ma’aikatan lafiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin kashi 95 na albashin ma’aikatan lafiya a sassan jihar, inda aka tsara sabon matakin ya fara aiki daga ranar 7 ga Satumba, 2026.

Gwamnatin ta ce, wannan sabon tsarin ya yi daidai da amincewar Gwamnatin Tarayya akan tsare-tsaren albashin fannin lafiya, musamman kan Tsarin Ƙarfafa Albashin Fannin Lafiya (CONHESS). Shugaban Ma’aikatan jihar, Shehu Baraya ne ya sanar da haka a wata wasiƙa mai ɗauke kwanan wata 10 ga Satumba, 2026.

An gabatar da ita ne kai-tsaye ga manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin jihar, masu taimakawa na musamman, manyan sakatarori, jagororin ma’aikatu, rassa da hukumomi, inda ya ce wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin bunƙasa harkokin fannin lafiya a jihar. A cewar gwamnatin, an yi gyaran albashin ne da nufin ƙarfafa harkokin fannin, inganta walwalar ma’aikata da samar da yanayin aiki mai kyau ga jami’an lafiya.

Akan haka ne gwamnatin jihar ta kirayi ma’aikatan lafiya da su kasance masu hoɓɓasa wajen gudanar da ayyukansu, nuna ƙwarewa da jajircewa akan ayyukan da aka ɗora musu. Haka kuma, ta umarci jagororin ma’aikatu da hukumomi da su sanar da batun ga ma’aikatan da hakan ya shafa da tabbatar da an aiwatar da baki ɗaya manufofin gyaran.

A ƙarƙashin sabon tsarin, jami’an lafiya ‘yan mataki na ɗaya zuwa na biyar, sun cancanci ƙarin ₦15,200, yayin da takwarorinsu da ba sa reshen, za su samu ƙarin ₦14,250. Ga ‘yan mataki na shida zuwa 12, alawus ɗinsu yana nan a ₦30,400 ga ma’aikatan lafiya sai ₦28,500 ga wasunsu. Su kuwa ‘yan mataki na 13 zuwa 15, za su samu ƙarin ₦32,300. Sai waɗanda ba su ba kuma za a musu ƙarin ₦30,400.

By Babaji

Leave a Reply