Uwargidan gwamnan Nasarawa ta jaddada muhimmancin tarbiyyar yara da mara wa APC baya

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Uwar gidan gwamnan jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullahi Sule ta yi kira na musamman ga mata a faɗin jihar da su ƙara ƙaimi wajen tarbiyyar ‘ya’yansu inda tace tarbiyya mai kyau ita ce ginshiƙin zaman lafiya da cigaban al’umma.

Tayi wannan kiran ne a ranar Litinin na makon da ake ciki a wani babban taron masu ruwa da tsaki na mata da aka gudanar a ɗakin taro na Banquet Hall, dake gidan gwamnati a Lafia babban birnin jihar.

Taron wanda ma’aikatar harkokin mata da cigaban al’umma ta shirya tare da haɗin gwiwar ofishin uwar gidan gwamnan, an yi shi ne da taken: “Mata masu ruwa da tsaki na tattaunawa don kare matasa da zaman lafiya gabanin 2027.”

A jawabin ta Hajiya Salifat Sule ta jaddada muhimmiyar rawar da uwaye ke takawa wajen kafa halayya.

“Mata su tabbatar da tarbiyyar ‘ya’yansu nagari domin su zama jakadu nagari na iyalansu, al’umma, jiha da ƙasa baki ɗaya.”

Ta bayyana cewa iyali shi ne matakin farko na tarbiyya, kuma ana iya magance zaman kashe wando na matasa da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran su munanan ɗabi’u idan uwaye suka ƙara himma wajen kula da tarbiyya.

Uwar gidan gwamnan ta kuma yi amfani da dandalin wajen neman goyon baya ga jam’iyyar APC mai mulki inda ta yi kira ga mata da su fito ƙwansu da kwarkwata su mara wa jam’iyyar baya a dukkan matakai a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

A cewarta cigaba da riƙe madafun iko daga matakin jiha zuwa tarayya da jam’iyyar APC ke yi, ya zama wajibi domin ɗorewar ayyukan cigaban da gwamnatin mijinta gwamna Abdullahi Sule da jam’iyyar suka shimfiɗa.

Gwamna Abdullahi Sule wanda shugabar ma’aikatan jihar, Dr. Abigail Waya ta wakilta shi ma ya ja hankalin mata game da siyasar cin hanci da sayen ƙuri’u.

“Ku yi hattara da ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa waɗanda ke yawo suna ruɗar jama’a da ɗan ƙaramin kuɗi don su cimma burinsu sannan su manta da su bayan zaɓe.”

Haka kuma sabuwar kwamishinar harkokin mata da cigaban al’umma kuma abokiyar shirya taron wato Hon. Rebecca Adamu Kpadji ta goyi bayan matsayin uwar gidan gwamnan.

Ta bayyana cewa manufar taron dabara ce.

“Manufar taron ita ce jawo mata daga sassa daban-daban na jihar su yi aiki tare a matsayin ƙungiya ɗaya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC baki ɗaya a zaɓen da ke tafe.” Inji ta.

Taron ya tattaro shugabannin mata da ƙungiyoyin siyasa da masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi 13 na jihar a matsayin wani ɓangare na shirin wayar da kai da wuri gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply