
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sheikh Ibrahim bin Adel Al Madani, ladani a Masallacin Haramin Makkah ya rasu a safiyar ranar Litinin bayan shafe shekaru 51 a duniya. Tashar Al-Ekhbariya ta Saudiyya ce ta tabbatar da labarin, wanda ya janyo alhini da miƙa saƙon ta’aziyya a kafafen sada zumunta.
Al Madani ɗaya ne daga cikin manyan ladanan babban masallacin na Makkah guda 24. Guda shida daga cikinsu na aikin kiran salla a kowace rana yayin sallolin farilla biyar.
Marigayin ya shahara ne da kiran sallar asubahi da kuma rera kabbarbarin Idi. Haka kuma, aikinsa ya haɗa da tabligh, wato maimaita kabbarorin liman domin isarwa ga sauran mamu a ko’ina a faɗin masallacin haramin domin sauraro.
An ruwaito cewa shi ne wanda ya yi kiran farko na sallar asubahin Litinin ɗin da ya rasu, kamar yadda wata ɗauka ta nuna acikin Haramain, wato sa’o’i kafin rasuwarsa. An yi masa jana’iza ne bayan sallar La’asar a babban masallacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, sannan aka binne shi a Maƙabartar Al Mu’alla.
Tuni dai Ma’aikatar kula da Harkokin Masallacin Harami da na Annabi (SAW), ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais suka miƙa gaisuwar ta’aziyyarsu ga rasuwar ladanin.
Tun a shekarar 1428 AH (2007-2008) ne ya fara aikin ladanci a Masallacin Al-Maddah, kana a 1439 AH (2017/2018) aka naɗa shi a matsayin ɗaya daga cikin ladanan harami.
