Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
An samu sabon sauyi a fagen siyasar Gombe, yayin da wasu fitattun makusantan ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, biyu suka fice daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar PDP.
Mutanen biyu, Hon. Ibrahim Adamu Muhammad, wanda aka fi sani da Uban Dawakin Gombe, da Alhaji Auwalu Alhassan, wanda aka fi sani da Chiburosi, sun kuma bayyana goyon bayansu ga takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a zaɓen gwamnan jihar na 2027.
Uban Dawakin Gombe tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Gombe ne, yayin da Chiburosi ya taba jagorantar ƙungiyar masu matsaran man gyada ta Jihar Gombe.
Ƙungiyar Pantamiyya Movement ce ta bayyana sauya shekar mutanen biyu cikin wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed ya sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, waɗanda suka sauya shekar sun ɗauki matakin ne bisa ga yadda suka yi imani da ƙwarewar Pantami wajen jagoranci, tafiyar da harkokin gwamnati da kuma irin rawar da ya taka a hidimar jama’a.
Sanarwar ta ce shigarsu PDP zai ƙara wa jam’iyyar da kuma ƙungiyar siyasar Pantami ƙarfi a faɗin jihar, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna na 2027.
“Matakin nasu wani ƙarin ƙarfi ne ga PDP da kuma ƙungiyar Farfesa Pantami da ke ƙara samun goyon baya a faɗin jihar Gombe,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta kuma ce sauya shekar za ta taimaka wajen ƙarfafa PDP a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar kuma jagoran jam’iyyar a Gombe, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo.
Ta bayyana Pantami a matsayin masani kuma mai hangen nesa, tana mai cewa tarihin ayyukansa na gwamnati, musamman a ɓangaren bunƙasa matasa da fasahar zamani, na daga cikin abubuwan da ke ƙara masa karɓuwa a tsakanin al’umma.
Sauya shekar ta zo ne a lokacin da manyan jam’iyyun siyasa a jihar ke ƙara tsaurara shirye-shiryensu da kuma ƙoƙarin faɗaɗa sansanoninsu gabanin babban zaɓen 2027.
Sabon sauyin dai na ƙara bayyana yadda fagen siyasar Gombe ke fara ɗaukar sabon salo yayin da ake ci gaba da fafatawa wajen neman goyon bayan masu ruwa da tsaki da kuma masu zaɓe a jihar.
