Ya kamata a riƙa hukunta masu tuƙin ganganci kamar yadda ake yi a kasashen ƙetare

Spread the love

Daga UNCLE LARABI

Yadda mutane ke tuƙin ganganci a Kano kai ka ɗauka a gidajen mahaukata suke zuwa a koya musu motar ko abin tuƙin, duk da kaso mai yawa na masu tuƙa motoci a Kano ‘sa giya, taka burki ne’. Ma’ana; koyo ne wajen abokansu ko kula da ƙafar direba, ba su zuwa ‘driving school’ a koya musu yadda ya kamata. 

Masu adaidaita sahu idan suka ga tirela har wani shige mata suke. Idan ka yi magana sauran fasinjan cikin adaidaita sahu ɗinsu za su ɗaure wa mai tuƙin gindi kan cewar ka fiye tsoro ran nan dai guda ɗaya ne.

Wallahi na sha Ina cikin adaidaita sahu na ga sun kusa mannewa ko motar za ta sha kwana, amma haka mai adaidaita sahu, don hauka da wauta zai ta bin tirelar bamba to bamba.

A nan akwai laifin hukumomi masu kula da tuƙi, duk da su ma masu tuƙin da nasu laifin. 

Akwai ‘distance’ da ake so a bari Ina jin kamar mita 100 ne tsakanin babbar mota da ƙananan ababen hawa, saboda za ta iya ribas ko juya wa wani abu zai iya faruwa. 

A nan laifin hukumomi ba sa sanar da masu tuƙin ko a rubuce akan ‘bill board’ ko a gidajen rediyo da talabijin, kawai su burinsu a yi laifi su kama mutum su karɓi cin hanci ya wuce.

Su kuma laifin mutane ba su sauraro ko karanta dokokin ko kuma nasihar da aka yi musu akan tuƙin, sannan da yawan masu tuƙin suna shan kayan da yake gusar da hankali, don wai su ji daɗin tuƙin, su yi rashin mutunci. 

Abinda zai ba ka mamaki shine, yadda wasu ke buge jami’an kula da titinan a cikin gari, ba a wajen gari ba, su mutu har lahira. Wannan wane irin rashin hankali ne da rashin imani? Mutum mai hankali da imani ko dabba ban zai iya bugewa ta mutu ba da gayya. 

Akwai wasu lokuta da idan Ina tuƙi na ɗauki wani sai ka ga an min ‘misbehaving’, wanda muke tare a motar ni fa nake tuƙi za ka ji yana cewa, ka taka shi mana ko ka buge shege mana. Na kan yi murmushi na ce, ka bari sai ka sayi taka motar sai ka yi hakan. Ni kam zaman lafiya nake nema kuma Ina addu’ar Allah ya raba ni da ƙarfen lafiya. 

Ya kamata gaskiya a gyara salon tuƙi a Kano, musamman na ganganci ko a rubuce a ‘bill board’ a dinga ankarar da mutane illar yin tuƙin ganganci, don yana kawo salwantar rayukan al’umma. 

Uncle Larabi marubuci ne a Kano

By ukarofi

Leave a Reply