‘Za mu garzaya Villa’, Iyayen yara 80 na Borno da ke hannun Boko Haram sun ba wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana shida ta ceto su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyaye da al’ummar yankunan Mussa da Lassa na Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta Jihar Borno sun yi barazanar zuwa Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja nan da kwana shida muddin ba a ceto yaransu ba da suke hannun ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Iyalan, waɗanda ke halin ƙunci na rashin ganin ‘ya’yansu a tsawon sama da kwanaki 130, sun fitar da wannan wa’adin gargaɗi ne a ranar Litinin yayin wata zanga-zanga akan abin da suka kira da halin ko-in-kula daga ɓangaren gwamnati a Askira-Uba. An yi garkuwa da yaran ne a wani babban atisaye da ‘yan ta’adda suka ƙaddamar a ranar 15 ga Mayu, 2026, inda iyaye da hukumomin makarantu suka ce al’amarin ya shafi yara 44 daga Gundumar Mussa da kuma wasu 36 daga wasu makarantu a Lassa.

Sannan, an sace yaran ne a ranar da aka sace sama da ɗalibai 40 da malamai a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo da ke Kudu maso yammacin Nijeriya. Amma daga bisani sun shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe kwanaki 56 a hannun ‘yan bindiga.

Shugaban iyayen ɗaliban Borno, Ishaku Suya, wanda ya jagoranci zanga-zangar, ya yi magiya cikin alhini ga Shugaba Bola Tinubu da ya umarci hukumomin tsaro su ceto ‘ya’yan nasu. Ya bayyana cewa, “za mu je titinan fadar shugaban ƙasa matuƙar bai ceto ‘ya’yanmu ba kamar yadda ya ceto ‘ya’yan Oyo. Saidai ka kashe mu ko ka bar mu da rai ko kuma ka ceto ‘ya’yanmu.”

Wata uwa mai suna Josephin Yohanna ta koka kan abin da ta kira da nuna bambanci daga ɓangaren yunƙurin gwamnati kan sace ɗaliban makaranta a shiyyoyi daban-daban. Ta ce, gaggauta ceto yaran Oyo shaida ce ta cewa Gwamnatin Tarayya tana da ikon warware matsalar yadda ake buƙata, tana mai ƙalubalantar yadda aka gaza aiwatar da irin haka a ƙoƙarin ceto ‘ya’yansu. “Mu ma ‘yan Nijeriya ne kamar kowa”, ta ƙara da faɗa.

Kamar haka shi ma Hakimin Lassa na riƙo, Wadzani Hammatu, ya koka kan sace yaran, waɗanda ya bayyana a matsayin masu ƙananan shekaru, wato daga “ɗaya zuwa uku”. Don haka ya yi kira ga gwamnatin da ta ceto yaran saboda al’amarin halin ƙuncin nasu ya fara ƙamari.

A nasa ɓangaren Sarkin Uba, Ali Sama’ila Mamza, ya ce sun bar komai a hannun Ubangiji, amma suna kira ga gwamnatocin tarayya, ta Borno da na ƙananan hukumomi da su yi hoɓɓasa wajen ganin yaran sun koma wa iyalansu cikin aminci.

Har ila yau, Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Askira/Uba da Hawul, Dakta Midala Usman Balami, ya yi alla-wadai da tsawon lokacin da yaran suka shafe a komar ‘yan ta’addar da rashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki a kai, yana mai cewa ya mika batun ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, sannan ya yi alƙawarin cigaba da bibiya domin ganin an samu nasara a kai.

By Babaji

Leave a Reply