Daga RABI’U SANUSI a Kano
Kamfanin Nestlé Milo tare da haɗin gwiwar tsohon kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Ahmed Musa, sun shirya gasar ƙwallon ƙafa ta yara ’yan ƙasa da shekaru 13 a Kano.
Kamfanin ya ce ya shirya gasar ce da nufin zaƙulo zaƙaƙuran yara masu baiwar ƙwallon ƙafa a faɗin Arewacin Najeriya.
Ya ce maƙasudin shirya gasar ta kusan tsawon mako uku shi ne domin a horar da yaran sannan a koya musu muhimmancin jajircewa, sadaukarwa da kuma fito da baiwar da suke da ita.
Da yake jawabi a lokacin buɗe gasar, wakilin kamfanin na Milo, Gilbert Tweneboah-Koduah, ya ce shirya gasar wani ɓangare ne na kamfanin na ganin cewa an yi amfani da wasanni wajen bunƙasa hazaƙar yaran, ba wai a fannin karatu kawai ba.
Ya ce sama da ƙungiyoyi 16 ne suka fafata a gasar yayin da gogaggun masu horarwa suka kasance tare da su.
Gilbert ya kuma ce koda yake an fafata sannan an fitar da zakaru amma babban burin gasar shi ne fito da yara masu hazaƙa daga cikin waɗanda suka fafata a cikinta, yana mai cewa suna fatan ganin cewa gasar za ta zama ta shekara-shekara a nan gaba.
Shi ma Ahmed Musa, wanda kuma Jakadan kamfanin na Milo ne, ya ce an ƙirƙiri gasar ce domin farfaɗo da ƙwazon yara da kuma zaƙulo masu baiwa daga cikinsu, kwatankwacin irin damar da ya ce shi ma ya samu lokacin yana yaro.
Ya kuma ce an zaɓo yaran ne saboda a samu damar gano masu baiwa domin a horar da su, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa nan gaba za a samu zakarun da za su buga wa Najeriya wasa daga cikinsu.
A cewar manajan filin wasan Ahmad Musa mai suna Musa Muhammad, an shirya gasar ce domin a jawo ƙananan yara a jika kasancewar akasarin gasar an fi shirya ta ne ga manya.
Ya ce “A kan haka ne kamfanin Milo ya ce mu nemo yara ’yan shekara takwas zuwa shekara 13 saboda su ma a ƙarfafa musu gwiwa a nuna ana yi da su”.
Ya ce a sakamakon gasar, kulob din Khamis Boy ne suka zo na ɗaya, sai BC Academy da suka zo ba biyu, sai Legacy da suka zo na uku, inda ya ce kowannensu sun samu kyaututtukan kuɗi masu yawa.
Ya kuma shawarci yaran da su dage da karatu sannan su haɗa shi da ƙwallon, yana mai cewa hakan zai ɗauke musu hankali daga abubuwa marasa kyau kamar shaye-shaye sannan ya sa su zama mutane na gari idan sun girma.
Shi ma manajan kulob ɗin Khamis Boy wanda suka zo na daya, ya ce sun samu tukwicin naira miliyan ɗaya, sannan ya gode wa kamfanin na Milo saboda ba su damar shiga gasar a fafata da su har suka kai ga nasarar.
Shi ma Dayo Adetoya, manajan kamfanin Milo a shiyyar Arewa maso Yamma, ya ce an shirya gasar na a haɗaka tsakanin kamfanin da Ahmed Musa domin fito da hazaƙar yara a fagen ƙwallon ƙafa sannan a ba su damar ƙarfafa mafarkinsu na zama zakaru a nan gaba.
Ya ce, “A sakamakon wannan gasar da aka shirya, na ga yaran da suna da alamun zama haziƙan ’yan ƙwallo a nan gaba. Wannan ne karo na farko da ake yin wannan haɗakar tsakanin kamfanin Milo da Ahmed Musa.
“Mun gano yara masu hazaƙa sosai kuma daga nan za mu ga hanyar da za mu bi domin ganin mun tallafa musu ta hanyar ba su horo har mafarkinsu ya kai ga tabbata saboda ganin cewa baiwarsu da ta bayyana a nan ba ta tafi a banza ba,” in ji Adetoya.
