Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da bibiyar shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, tare da ƙoƙarin tabbatar da an yi adalci a lamarin.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau yayin taron Maulidin Annabi Muhammad (SAW) da Jami’atu Sankwari ta shirya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Bazullahi Kabara, inda ya yi tsokaci kan shari’ar Sheikh Abduljabbar.
“Insha Allah, Gwamnatin Jihar Kano tana bibiyar shari’ar, kuma Insha Allah Gwamnatin Jihar Kano za ta tsaya ta tabbatar an yi adalci, wanda duk ‘yan’uwa da al’ummar Musulmi za su yi farin ciki.” Inji Shi
Ya ƙara da cewa adalci shi ne ginshiƙin haɗin kan al’umma, yayin da ƙaunar juna ke ƙara tabbatar da wannan haɗin kai.
A cewarsa, “Adalci shi yake tabbatar da haɗin kai, kuma ƙaunar juna ita take tabbatar da haɗin kai.”
Mataimakin Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da zaman lafiya, tare da guje wa duk wani abu da ka iya kawo rabuwar kai.
“A matsayinmu na Musulmi, mu ci gaba da zaman lafiya. Mu ci gaba da addu’a, da dukkan abin da ya fi ƙarfin ɗan Adam, domin bai fi ƙarfin Allah ba,” in ji Mataimakin Gwamnan.
Jawabin na Mataimakin Gwamnan ya zo ne a yayin da ake ci gaba da shari’ar Sheikh Abduljabbar, inda ya jaddada cewa gwamnati na bibiyar lamarin tare da fatan ganin an tabbatar da adalci da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
