Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya ƙalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan alkawarin da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023 na inganta samar da wutar lantarki a Nijeriya. Makinde ya ce bai kamata Tinubu ya nemi wa’adi na biyu ba idan har ba a magance matsalar wutar lantarki ba.
Makinde ya ce Tinubu ya taɓa bayyana cewa idan ba a gyara matsalar wutar lantarki ba, bai kamata ’yan Nijeriya su sake zaɓensa a wa’adi na biyu ba, inji shi. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani babban taron kaɗe-kaɗe da aka gudanar a filin wasa na Lekan Salami da ke Ibadan, inda ya kuma kare amfani da janaretocin dizal wajen kunna fitilun tituna a jihar.
Ya ce rashin tabbas wajen samun wutar lantarki daga babbar hanyar samar da wutar ƙasa ne ya tilasta wa gwamnatin jihar amfani da janareto. A cewarsa, da a ce ana samun ingantacciyar wutar lantarki a ƙasa, gwamnatocin jihohi ba za su kashe kuɗaɗe wajen sayen dizal domin gudanar da wasu muhimman ayyuka ba.
Sai dai an samu saɓanin fahimta kan ainihin ma’anar kalaman Tinubu na 2023. Makinde da Peter Obi sun fassara kalaman a matsayin alkawarin cewa Tinubu ba zai nemi wa’adi na biyu ba idan ya gaza inganta wutar lantarki. Sai dai mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ƙalubalanci wannan fassarar, yana mai cewa kalaman shugaban suna da sharaɗi.
A gefe guda, Gwamnatin Tarayya ta ce tana ɗaukar matakai domin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar ɓangaren wutar lantarki. Ma’aikatar Lantarki ta bayyana shirye-shiryen zuba ƙarin jari domin ƙarfafa tsarin wutar lantarki na ƙasa, tare da inganta samarwa, watsawa da rarraba wutar lantarki.
Sai dai Makinde ya ce yadda gidaje, ’yan kasuwa da gwamnatocin jihohi ke ci gaba da dogaro da madadin hanyoyin samar da wuta na nuna cewa har yanzu akwai matsalar da ba a warware ba. Ya ce ya kamata a auna gwamnatin Tinubu da ma’aunin da shugaban ƙasar da kansa ya samar a lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2023.
