Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya gargadi ’yan siyasa da masu riƙe da mukaman gwamnati da su guji amfani da kuɗaɗen jama’a da aka samu ta hanyar rashawa wajen ɗaukar nauyin zuwa wuraren ibada na Makka da Kudus, yana mai cewa Allah ba Ya karɓar ibadar da aka gudanar da kuɗin da aka samu ta hanyar haram.
Sultan ya yi wannan gargaɗin ne ranar Laraba a Abuja, yayin buɗe taron masu ruwa da tsaki da Majalisar ƙasa ta Addinai (NIREC) ta shirya, inda ya buƙaci shugabannin addinai su ƙara haɗa kai da hukumomin yaƙi da rashawa wajen tunkarar matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar.
Da yake magana a wajen taron, Sultan ya ce shugabannin addinai na da nauyin yin yaƙi da rashawa tare da tallafa wa hukumomi irin su Hukumar Yaƙi da Yiwa Tattalin Arziƙi Zagon ƙasa (EFCC) wajen tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifi sun fuskanci hukunci.
Ya ce ba za a iya amfani da kuɗin da aka sace wajen gudanar da ibada a matsayin hanyar samun karɓuwar aikin ibadar ba, yana mai jaddada cewa kuɗin da aka samu ta hanyar rashawa ba ya zama halal saboda kawai an yi amfani da shi wajen biyan kuɗin Hajji ko wasu ayyukan ibada.
Sultan ya kuma buƙaci EFCC ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ake zargi da aikata rashawa, ba tare da la’akari da matsayinsa na siyasa, addini ko dangantakarsa da wasu mutane ba. Ya ce babu wanda ya kamata a kare shi daga fuskantar doka saboda matsayinsa a cikin al’umma.
Ya kuma yi kira ga hukumomin yaƙi da rashawa da su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma bakin siyasa ba, tare da buƙatar shugabannin addinai su tallafa wa duk wani yunƙuri da ke da nufin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da ɗabi’a mai kyau a cikin al’umma.
A kan haɗin kan ƙasa, Sultan ya bayyana NIREC a matsayin wata muhimmiyar kafa da ke samar da dama ga Musulmi da Kirista su tattauna tare, su fahimci juna, tare da ƙarfafa zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Ya buƙaci shugabannin addinai su wuce matakin jure wa juna kawai, su koma ga samun cikakkiyar fahimtar juna domin samun zaman lafiya da haɗin gwiwa mai ɗorewa.
Sultan ya kuma gargadi malaman addini da su kula da kalaman da suke furtawa a kan mimbari, musamman lokacin zaɓe, yana mai cewa ya kamata su yi addu’a ga shugabannin ƙasa maimakon amfani da wuraren ibada wajen tayar da rarrabuwar kawuna ko kai hari ga masu riƙe da mukaman gwamnati.
Ya yaba wa tsohon Babban Sakataren NIREC, Farfesa Cornelius Omonokhua, bisa gudummawar da ya bayar a tsawon shekaru takwas da ya yi yana jagorantar majalisar, yana mai cewa ya taimaka wajen mayar da NIREC wata muhimmiyar kafa ta tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Sultan ya kuma buƙaci mahalarta taron da su tattauna batutuwan ƙasa cikin gaskiya da faɗin albarkacin baki, tare da guje wa yaɗa jita-jita idan suka koma garuruwansu.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Yaƙi da Rashawa tsakanin Addinai (IAAC), Farfesa Adedibu Ojerinde, ya bayyana kundin yaƙi da rashawar addinai a matsayin wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin EFCC da shugabannin addinai domin tunkarar matsalar ɗabi’a da rashawa a ƙasar.
Ojerinde ya ce an ƙirƙiri kundin ne domin amfani da mimbari da sauran wuraren ibada wajen wayar da kan jama’a kan illolin rashawa, tare da dogaro da koyarwar Littafi Mai Tsarki da Alƙur’ani.
Ya ce an fara ƙaddamar da kundin a shekarar 2014, sannan aka sake ƙaddamar da shi a watan Janairun 2024 a ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda daga baya aka faɗaɗa shi domin tunkarar sabbin ƙalubale da suka haɗa da matsalolin matasa, laifukan yanar gizo da kuma safarar kuɗaɗen haram a wasu cibiyoyin addini.
An gudanar da taron ne tare da halartar shugabannin Musulmi da Kirista, jami’an gwamnati, jami’an tsaro da ’yan jarida.
