Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce shari’ar da yake fuskanta ta sa ya sake duba alaƙar da ke tsakaninsa da wasu daga cikin abokansa da abokan aikinsa.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na ɗ, inda ya ce wasu daga cikin mutanen da ya taɓa mara wa baya sun yi shiru a lokacin da yake cikin wannan hali. Ya ce wahalhalun da ya fuskanta a watannin baya sun koya masa darussa game da rayuwa da kuma yadda ake gane haƙiƙanin alaƙar mutane a lokacin tsanani.
Tsohon gwamnan na fuskantar shari’a kan zargin halasta kuɗaɗen haram da kuma karkatar da kadarorin gwamnati. Hukumar ICPC ce ke tsare shi tun ranar 19 ga Fabrairu, bayan hukumar EFCC ta sake shi. El-Rufai ya ce bai yi nadamar goyon bayan mutanen da ya taɓa mara wa baya ba, yana mai cewa ya yi hakan ne bisa imaninsa, tarbiyyarsa da kuma abin da lamirinsa ya nuna masa.
Ya kuma ce ba ya neman ramuwar gayya ko hukunta duk wanda ya kasa mara masa baya a halin da yake ciki, yana mai cewa zai bar hukunci na ƙarshe ga Allah. Ya ce abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne kasancewa cikin kwanciyar hankali da lamirinsa da kuma imaninsa, yayin da lokaci zai bayyana yadda mutane suka yi amfani da zaɓin da suka ɗauka.
A saƙon na El-Rufai, mai ratsa zuciya, ya ce, “wasu mutane sun nuna damuwa game da abin da suke ganin kamar shirun da wasu daga cikin abokan aikina, abokaina da ’yan uwana suke yi a halin da nake ciki yanzu, musamman waɗanda a baya na fito fili na mara wa baya ko kuma muka kasance muna da kusanci. Ra’ayina game da wannan lamari abu ne mai sauƙi, kuma ga shi nan, A tsawon rayuwata, na yi ƙoƙarin yin abin da zan iya domin abokan aikina da abokaina, iyalina da kuma bil’adama baki ɗaya, bisa jagorancin imanina na Musulunci, tarbiyyar Arewa da na taso a cikinta, ƙa’idojina na kaina, kuma sama da komai, lamirina.
“A tsawon shekaru, na tsaya tare da mutane, kuma na goyi bayan wasu manufofi da na yi imani da su, wani lokaci a cikin yanayi mai wahala da kuma tare da babban sadaukarwar kaina. Ban yi hakan ne saboda ina tsammanin yabo, godiya ko za a rama min abin da na yi ba; na yi hakan ne saboda na yi imanin cewa abin da ya dace ne. Waɗannan zaɓi ne da na yi da kaina, kuma ni ne ke da alhakinsu.
“Haka kuma, mutanen da na taɓa mara wa baya suna da ’yancin yin zaɓinsu na kansu yanzu da yanayi ya sauya. Wasu na iya yin magana; wasu kuma su yi shiru. Wasu ma na iya musanta dangantakarmu ko kuma su yi ƙoƙarin sake fasalta tarihin abin da ya faru tsakaninmu. Dalilansu nasu ne, kuma ba na son in yi musu hukunci kawai saboda yadda suka mayar da martani ya bambanta da abin da wasu ko ma ni kaina muka yi tsammani.
“Wahala tana da wata hanya ta bayyana ainihin dangantakar mutane. Abin da na koya a cikin wannan mawuyacin lokaci na ’yan watannin da suka gabata na iya sa ni, cikin nutsuwa kuma ba tare da nadama ba, in sake duba yanayin wasu daga cikin dangantakata da kuma irin abubuwan da waɗanda suke kallona a matsayin abin koyi suke tsammani daga gare ni. Wannan ba zargi ba ne, kuma ba hukunci ba ne; wani ɓangare ne kawai na fahimtar mutane da rayuwa cikin haske da zurfi.
Ba na da nadamar tsayawa tare da mutane ko goyon bayan wasu manufofi a lokacin da na yi imanin cewa yin hakan shi ne daidai. Haka kuma, ba na jin haushin duk wanda ya zaɓi kada ya yi mini irin abin da na yi masa. Na fi son in kasance mai aminci ga ƙa’idojin da suka jagoranci halina da ayyukana, maimakon in bari halayen wasu su sa na sauya waɗannan ƙa’idoji.
Game da duk wani rashin adalci, rashin godiya ko cutarwa da aka yi mini, ba na neman ɗaukar fansa ko ramawa. Allah Maɗaukakin Sarki ne ke da cikakken ikon yin hisabi, kuma gare Shi na bar wannan hukunci – a duniya da kuma Lahira.
A ƙarshe, kowannenmu dole ne ya rayu da sakamakon zaɓin da ya yi, kuma tarihi zai yanke hukuncin da ya ga ya dace. Abin da ya fi damuna shi ne in kasance cikin kwanciyar hankali da lamirina, kuma sama da komai, in kasance cikin salama da Allah Maɗaukakin Sarki. Nasir Ahmad El-Rufai, 23 ga Satumba, 2026”
