Medina Dauda ta zama kakakin ABER

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An naɗa fitacciyar ’yar jarida kuma gogaggiyar mai gabatar da shirye-shiryen rediyo da talabijin, Hajiya Medina Dauda Nadabo, a matsayin Daraktar Sadarwa da Harkokin Jama’a ta Hukumar Tattaunawa Kan Tattalin Arzikin Teku Na Afirka, wato Africa Blue Economy Roundtable (ABER).

An bayyana naɗin ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 15 ga Satumba, 2026, wadda Shugaban Hukumar kuma Babban Daraktan ABER, kana Shugaban Kwamitin Amintattu na BRACED Tourism Promotion and Development Initiative (BTPDI), Dakta Piriye Kiyaramo, ya sanya wa hannu.

A cewar wasiƙar, an yi la’akari da Nadabo ne bisa dogon tarihin aikinta a aikin jarida, musamman aikin watsa labarai, inda ta shafe sama da shekaru 40 tana aikin jarida da watsa shirye-shirye na ƙasa da ƙasa.

Haka kuma, ta yi aiki a matsayin Mai Kula da Ofishin Hausa da Jami’ar Shirye-shirye na Sashen Nijeriya na Muryar Amurka (VOA) tun daga shekarar 1998, a sassan shirye-shiryen Turanci da Hausa.

A sabon matsayinta, Nadabo za ta jagoranci dabarun sadarwa na ABER, harkokin tambarinta da sanarwar hukumarta, tare da zama kakakinta.

Za ta kuma kula da hulɗar hukumar da kafafen yaɗa labarai da jama’a, tare da kula da shafin intanet da kafafen sada zumunta na ABER.

Daga cikin sauran nauyin da aka ɗora mata akwai kula da hulɗa tsakanin ABER da hukumomin gwamnati, ofisoshin jakadanci da sauran masu ruwa da tsaki.

Haka kuma, za ta jagoranci ayyukan wayar da kan jama’a da neman goyon baya ga mata a fannin Tattalin Arzikin Teku, kula da sadarwar cikin gida da wallafe-wallafen hukumar, tare da jagorantar yaɗa shirye-shiryen ABER da lambobin yabo da take bayarwa.

By ukarofi

Leave a Reply