Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya (SGF), Babachir Lawal, ya koma jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), watanni uku bayan ya yi murabus daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bisa zargin cewa an yi magudi a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Lawal ya sanar da komawarsa jam’iyyar NDC a hukumance ne a Abuja ranar Talata, inda shugabannin jam’iyyar adawar suka tarbe shi gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Tsohon SGF ɗin ya kuma bayyana goyon bayansa ga tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar da ya ƙunshi Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, yana mai cewa haɗin kansu wata dama ce ta magance wasu daga cikin ƙalubalen da ke addabar ƙasar.
Da yake jawabi bayan karɓar sa a matsayin ɗan jam’iyyar, Lawal ya ce ya kamata ’yan Nijeriya da ke damuwa da matsalolin rashin tsaro, yunwa, jahilci, cututtuka da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, su mara wa jam’iyyar NDC baya.
Ya ce, “Duk wani ɗan Nijeriya da ke da kishin ƙasa da kuma tausayi ga wahalhalun da ake fuskanta a ƙasar nan, da suka haɗa da rashin tsaro, yunwa, jahilci da cututtuka, ba zai samu wani zaɓi ba face ya shiga jam’iyyar da ke wakiltar makomar ƙasa, wadda Peter da Kwankwaso suke a matsayin ’yan takararta.”
Lawal ya bayyana cewa ya yi imanin ya zama wajibi ’yan Nijeriya su goyi bayan jam’iyyar NDC domin cimma burinta na kafa Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa, yayin da Rabiu Kwankwaso zai zama mataimakinsa bayan zaɓen 2027.
Ya kuma bayyana kyakkyawan fata game da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, yana mai cewa magoya bayanta za su yi ɗokin isa ranar 29 ga Mayu, 2027, wadda ya bayyana a matsayin ranar da za a yi bikin abin da ya kira wata gagarumar nasara domin amfanin ƙasa da kuma tsararraki masu zuwa.
Da yake tarbar tsohon SGF ɗin zuwa jam’iyyar, Jagoran ƙasa na NDC, Sanata Seriake Dickson, ya bayyana Babachir Lawal a matsayin ƙwararren mai tattara magoya baya da kuma ɗan gwagwarmayar siyasa, wanda ya taka muhimmiyar rawa a siyasar Nijeriya.
Dickson ya ce ƙwarewar Lawal ta wuce matsayin da ya taɓa riƙewa na Sakataren Gwamnatin Tarayya, yana mai bayyana shi a matsayin mutum mai ƙwarewa sosai wajen tattara magoya bayan siyasa.
Ya ce Lawal zai taka rawar jagoranci a cikin jam’iyyar, tare da kula da ayyukan NDC da yaƙin neman zaɓenta a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.
A cewar Dickson, ana kuma sa ran Lawal zai taimaka wajen warware matsaloli tare da bayar da shawarwari da jagoranci ga ’yan takarar jam’iyyar da kuma ayyukan yaƙin neman zaɓe a faɗin yankin.
Komawar Lawal jam’iyyar NDC ta biyo bayan murabus ɗinsa daga ADC kimanin watanni uku da suka gabata.
Tsohon SGF ɗin ya zargi jam’iyyar da gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa cikin wata hanya da ya bayyana a matsayin mai cike da kura-kurai, yana mai cewa an yi magudi domin fifita tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
A cikin wata sanarwar murabus da ya wallafa a shafinsa na Facebook a lokacin, Lawal ya ce ba zai iya ci gaba da zama a jam’iyyar da yake ganin an lalata tsarin zaɓen fidda gwaminta ba.
Ya yi zargin cewa an sauya sakamakon zaɓen domin fifita Atiku da magoya bayansa, yana mai cewa an maye gurbin waɗanda aka ayyana a matsayin waɗanda suka yi nasara, har ma a wasu wuraren da aka gudanar da zaɓe.
