(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
Ko me Bollywood take yi wa nata jaruman?
A Indiya ma, musamman a masana’antar fina-finan Mumbai, an gina ƙungiyoyi da asusun jin daɗi da suka dade suna kula da matsalolin masu fasaha. Cine & TV Artistes’ Association (CINTAA), wadda aka yi wa rajista a matsayin ƙungiyar kwadago, ta bayyana a kundinta cewa daga cikin manufofinta akwai neman tallafin mambobi idan suka fuskanci rashin lafiya, nakasa, tsufa ko mutuwa.
Ba nan ne kawai ba. CINTAA ta bayyana cewa tana da hanyoyin tallafin gaggawa na lafiya ga wasu mambobi, sannan akwai tsarin taimakon kuɗi ga waɗanda suka cancanta. Kundinta ya kuma tanadi haɗin gwiwa da asibitoci da sauran ayyukan jin daɗi.
A gefe guda kuma, Cine Artistes Welfare Trust, wanda ke aiki tare da CINTAA, ya bayyana cewa yana ba da tallafin jinya a asibiti, taimakon tiyata da rashin lafiya ta gaggawa, tallafin kuɗi ga masu fama da rashin lafiya ko tsufa, da kuma tallafin ilimi ga ‘ya’yan masu fasaha. Shafin trust ɗin ya ce sama da masu fasaha 9,000 aka tallafawa, kuma an raba fiye da ₹2.15 crore a tsawon ayyukansa.
Haka ma All Indian Cine Workers Association ta bayyana cewa daga cikin fa’idodin kasancewa mamba akwai ƙoƙarin samar da fansho, taimakon lafiya da tallafin karatun ‘ya’yan mambobi masu bukata.
Wannan ba yana nufin Bollywood ba ta da matsaloli ba. Har yanzu akwai tsoffin jarumai da suke shiga matsalar kuɗi ko rashin lafiya, kuma wani lokaci sai abokan sana’a su fito su taimaka. Amma bambancin da ya kamata a koya shi ne cewa taimakon mutum ɗaya daga wani babban jarumi ba shi ne cikakken tsarin walwala ba; tsarin ƙungiya da asusun jin daɗi shi ne yake rage dogaro da irin wannan agaji.
To, ina Najeriya take a wannan batu?
Za mu kai ƙarshen wannan rahoton a mako mai zuwa da yardar Allah.
To, ina Najeriya take a wannan batu?
Abin mamaki shi ne cewa wannan tambayar ta fara samun amsa a Najeriya a kwanakin nan. A ranar 27 ga Agusta 2026, wato kwanaki kaɗan kafin rasuwar Zee Diamond, an ƙaddamar da Society for the Advancement of Entertainment and Trust, wani sabon shiri da aka ce an tsara shi domin inganta walwala, lafiya, inshora da tsaron kuɗi na dogon lokaci ga masu sana’ar nishaɗi. An ƙaddamar da shi da kuɗin farawa na Naira biliyan ɗaya, tare da burin kaiwa Naira biliyan biyar.
Taken shirin ma yana ɗauke da ma’anar sa, wato “Life After the Art.” Ma’ana, abin da ake son fara magana a kai shi ne abin da ke faruwa da mai fasaha bayan ya gama aikinsa ko kuma lokacin da ya kasa ci gaba da yin aiki. Masu shirin sun ce manufar ita ce a rage dogaro da kiran jama’a lokacin da mai sana’ar nishaɗi ya kamu da rashin lafiya ko ya shiga matsalar kuɗi.
A wurin ƙaddamar da shirin, Femi Falana SAN da sauran masu ruwa da tsaki sun yi kira da a samar da tsarin inshora da tallafi mai ɗorewa domin masu nishaɗi. Wannan magana ta samu ƙwarin gwiwa ta kowane ɓangare. Kuma idan aka duba ta bayan mutuwar Zee Diamond, domin kwanaki kaɗan kafin mutuwarta an riga an yi magana a ƙasa baki ɗaya kan yadda masu fasaha ke shiga matsalar rashin lafiya da rashin kuɗi wanda rashin kariya irin wannan ke bayyanawa.
A ɓangaren Nollywood ma, akwai wani abu da ya nuna cewa matsalar ba ta tsaya a iya Kannywood ba. Shugaban Actors Guild of Nigeria, Abubakar Yakubu, ya yi kira ga ‘yan wasan kwaikwayo su yi amfani da tsarin inshorar lafiya na guild ɗin, su yi gwaje-gwajen lafiya akai-akai, yana mai cewa tsarin ya ba mambobi damar samun kulawar lafiya da binciken gano matsaloli tun da wuri. Ya kuma ce wasu mambobin ba sa amfani da damar da suke da ita saboda suna ganin suna cikin koshin lafiya.
Wannan yana nuna cewa a Najeriya ma an fara fahimtar cewa mai fasaha ba zai iya dogaro da shahara kaɗai ba. Yana buƙatar inshora, kulawar lafiya, tsaro na kuɗi da tsarin da zai kula da mutum kafin ya kai ga neman taimako a bainar jama’a.
Amma me ya sa wannan yake da muhimmanci musamman ga Kannywood?
Saboda Kannywood ba ƙaramar masana’anta ba ce da za a ce jarumai kaɗan ne kawai ke aiki a cikinta. Tana da dubban masu aiki kai tsaye da waɗanda aikinsu ke ke zama tubali ga duk wani aiki da zata yi, duk da cewa ba a cika sanin su ba. Akwai kuma waɗanda muka saba gani ko ji ko karanta sunayensu daga jarumai zuwa daraktoci, masu ɗaukar hoto, editoci, masu kayan sawa, masu kwalliya da sauran ma’aikatan da ba a cika ganin fuskokinsu ba. Idan ɗaya daga cikin waɗannan mutane ya kamu da rashin lafiya, kuma ba shi da wani tsarin inshora ko asusun jinya da zai iya dogaro da shi, to nauyin zai koma ga iyalansa, abokansa ko jama’a.
Zee Diamond ta nuna yadda wannan tsarin yake aiki a zahiri. Lokacin da jinya ta tsananta, sai aka nemi jama’a su taimaka. ‘Yan Kannywood suka shiga, ‘yan uwa suka shiga, masoya suka shiga, aka tara miliyoyin naira. Wannan ya nuna cewa akwai tausayi da haɗin kai a masana’antar. Amma kuma ya nuna cewa haɗin kan mutane ba zai maye gurbin tsarin hukuma ba.
Domin wata rana ba Zee Diamond ce za ta iya fuskantar irin wannan matsala ba. Za ta iya zama jarumin da ya yi suna a shekarunsa na baya, ko wata jarumar da ta shahara a wani dogon shiri, ko ma wani ma’aikacin da masu kallo ba su san sunansa ba amma ya kwashe shekaru yana aiki a bayan kyamara.
Shin abin da ya faru da Zee Diamond ya kamata ya zama lamarin da zai zaunar da Kannywood a sabon teburi?
Watakila wannan shi ne babban darasin da mutuwarta ta kamata ta bari. Ba wai a yi ta tuna Maman Bintalo ne kawai a matsayin jarumar Labarina ba, ko a dinga wallafa hotunanta da addu’o’in Allah Ya jikanta ba. Ya kamata rasuwarta ta sa masu ruwa da tsaki a Kannywood su zauna su tambayi kansu abin da za su yi wa mutumin da ya yi musu hidima idan ranar da ya kasa yin aiki ta zo.
Shin ya kamata a kafa asusun jinya na Kannywood wanda jarumai da masu shirya fina-finai za su rika bayar da gudunmawa a kai tun suna cikin lafiya? Shin ya kamata a samu inshorar lafiya ta masana’antar da za a iya bai wa jarumai da sauran ma’aikata a farashi mai sauƙi? Shin masu shirya fina-finai za su iya ware wani kaso daga kuɗin aikin domin walwalar ma’aikatan da suke aiki da su? Shin akwai bukatar a yi cikakken rajistar masu sana’ar fim domin a san waɗanda ke cikin masana’antar da kuma irin kariyar da suke samu?
Sai kuma babba daga cikin batutuwan da ya kamata a tattauna matuƙar ana so masana’antar ta fara jin ƙamshin tsari da ci gaban da manyan masana’antun nishaɗi ke samu ita ce, idan fim ɗin da jarumi ya yi ya ci gaba da samun masu kallo da kuɗi shekaru bayan ya karɓi kuɗin aikinsa, shin bai kamata a samu wata hanyar da zai ci gaba da amfana da aikinsa ba?
Wannan za a iya ganinsa tamkar ba abu mai muhimmanci ba, saidai ga irin wannan tsarin za a iya samun jarumai da ƙoƙarin ganin sun bada dukka hankali da iyawarsu kan fim. Wani lokacin ma za su iya ƙoƙarin gina kansu ta hanyar neman gwarewa daga masana ko ɓata fiye da lokacinsu da aka nema wurin ganin rawar da suka taka ta kai matakin ƙarshe, ba kuwa don komai ba sai kwaɗayin fim ɗin ya jima yana samun tagomashi saboda burinsu na ganin ya zame masu jarin da zasu samu ribar sa har bayan sun bar fim.
