
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo gida Nijeriya bayan wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jagorantar tawagar ƙasar a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) karo na 81 a Amurka.
A ranar 20 ga Satumba ne Shettima ya bar Nijeriya bisa umarnin Shugaba Tinubu domin wakiltar Nijeriya a taron wanda ya haɗa jagororin ƙasashe da kuma gabatar da matsayar Nijeriya akan muhimman batutuwan da suka shafi ƙasar, shiyya da kuma muhimmancinsu a matakin duniya. An gudanar da taron ne na wannan shekara mai taken, “Restoring trust, managing transformation: A United Nations that delivers for all.
A yayin kasantuwarsa a taron, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya gabatar da jawabin ƙasa a madadin Shugaba Tinubu, inda ya yi amfani da fagen wajen jaddada matsayar Nijeriya akan gyare-gyaren cibiyoyin ƙasa-da-ƙasa, musamman majalisar tsaron MƊD. A babban muhawarar, Shettima ya sabunta kiran Nijeriya ga samar wa Afirka wakilci na dindindin a majalisar tsaron tare da wasu muhimman gyare-gyare da nufin faɗaɗa wakilcin MƊD ta yadda za ta dace da halin da duniya take ciki a yau.
Tawagar Nijeriyar ta kuma bayyana matsayar ƙasar akan ƙarfafa lamuran ci-gaban ta fuskar kuɗaɗe, sauyin yanayi, zaman lafiya da tsaro, samun damarmakin amfani da fasaha da kuma haɗin kai tsakanin ƙasashe. Haka kuma, zuwan Shettima taron ya bai wa Nijeriya damar ganawa da jagororin ƙasashen duniya, ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa da abokan hulɗa akan muhimman al’amuran da suka shafi ci-gaban tattali da harkokin difulomasiyya da dai sauransu.
