
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya kammala hutunsa na shekara yayin da ya bar Paris, ƙasar Faransa inda ya ƙudiri aniyar dawo wa gida Nijeriya.
Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata sanarwa a ranar Talata. Ya bayyana cewa, ana tsammanin jirgin Shugaban ƙasar ya iso filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas a wannan yammacin.
Ya ce, Shugaban ya zaɓi ya fara sauka a Legas karrama tunawa da Cif MKO Abiola, wanda ya rasu yayin fafutukar dimukraɗiyyar Nijeriya. Ya ƙara da cewa a zaman nasa na Legas, shugaban zai kuma shiga tattaunawa da jagororin siyasa da abokan hulɗa kan shirye-shiryen zaɓen 2027.
A ranar 30 ga Agusta ne Shugaba Tinubu ya bar Nijeriya ya tafi Landon inda ya shafe mako guda, kana daga nan ya garzaya Paris.
A zamansa na Paris, Tinubu ya gana da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Attajiri Mista Vincent Bollore kan muhimman al’amuran shugabanci.
