
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan bindiga a Jihar Neja, sun sace manoma a wasu hare-hare da suka ƙaddamar a Ƙaramar Hukumar Mariga, inda shugaban ƙaramar hukumar ya ce jimillar mutanen da aka yi awon-gaba da su sun kai 47. Ya kuma ya ce masu garkuwar sun buƙaci ba su Naira miliyan biyu ga kowane ɗaya daga cikinsu a matsayin kuɗin fansa.
Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya auku ne a lokacin da mutanen suke tsaka da aikin nome gyaɗa a gonakinsu da ke Tungan Rimi a Gundumar Ma’undu-Beri ta ƙaramar hukumar. An ruwaito cewa, a ranar Asabar ne al’amarin ya faru, inda maharan suka kuma yi garkuwa da wasu mutane da ke aiki a wasu gonaki a kusa da wajen.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Mariga, Alhaji Aliyu Bagga Muhamadu ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da manema labarai ta tarho, inda ya ce ɗaya daga cikin mata acikin waɗanda aka sacen ta haihu a hannun ‘yan bindigar. A cewarsa, masu garkuwar sun kira wasu daga cikin ‘yan uwan manoman, inda suka buƙaci a biya miliyan 2 ga kowannensu domin sako su.
Sannan, ya ce an tura jami’an tsaro tare da haɗin-gwiwar ‘yan bijilante domin ceto mutanen. Ya ce haɗakar jami’an ta yi ba-takashi da ‘yan bindigar a yankin ƙauyen Alibani bayan sun wuce ta Kasuwan Garba da Biri, inda wani ɗan bijilante ya samu raunuka.
Saidai, Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayar da wani adadi, inda ta tabbatar da cewa mutane 20 ne aka sace a ƙauyen Mukura da ke Gundumar Kasuwan-Garba fa Mariga. Kakakinta, SP Wasiu Abiodun a wata sanarwa, ya ce an ruwaito musu labarin ne a ranar 28 ga Satumba, idna ya ce an sace mutanen ne da misalin ƙarfe 3 na rana a ranar 27 ga Satumba.
