Kwalliya ko barazana? Lokacin da neman hasken fata ke zama haɗari

Spread the love

(Corticosteroids a kayan kwalliya)

Daga AISHA ASAS

Akwai wani irin farin ciki da mace kan ji idan ta fara amfani da sabon cream, sannan cikin ’yan kwanaki ta duba jikinta ta ga abin da take kira canji. Wataƙila launin fata ya fara sauyawa, wasu tabo sun yi kamar sun ragu, fata ta yi laushi, sai zuciya ta ce, “Na samu abin da nake nema.” Daga nan sai a ƙara amfani da shi, ko ta ba ƙawarta shawara ta saya, domin idan cream ya yi aiki da sauri, me zai sa a nemi wani?

Amma a duniyar kula da fata, akwai wata tambaya da ta fi muhimmanci fwato me ya sa ya yi aiki da sauri haka?”

Wannan tambayar ce ta kamata mace ta fara yi idan ta lura wani cream yana sauya yanayin fatarta cikin gaggawa, musamman idan ba ta san ainihin sinadaran da ke cikinsa ba. Domin wasu daga cikin abubuwan da kan sa cream ya ba da irin wannan sakamako ba kayan kwalliya kawai ba ne. Wasu magunguna ne masu ƙarfi da likitoci ke amfani da su wajen magance takamaiman cututtukan fata, amma idan aka yi amfani da su ba tare da kulawar ƙwararren ma’aikacin lafiya ba, musamman a manyan sassan jiki ko na dogon lokaci, abin da aka fara ɗauka a matsayin kwalliya na iya zama wata matsala ta daban.

A nan ne corticosteroids suka shiga cikin labarin.

Corticosteroids rukuni ne na magunguna da ake amfani da su wajen rage kumburi da magance wasu cututtukan fata. Saboda ƙarfinsu, wasu daga cikinsu na iya kawo sauyi cikin sauri a yanayin fata. Wannan ne yake sa wani lokaci mace ta ɗauki cream a matsayin mai kyau sosai saboda kawai ta ga canji cikin ɗan lokaci. Amma irin wannan canjin ba shi ne kaɗai abin da ya kamata a kalla ba. ƙarfi, tsawon lokacin amfani, inda ake shafawa da kuma ko ana amfani da shi bisa umarnin likita duk suna da muhimmanci.

A ƙa’idar NAFDAC kan kayayyakin bleaching, hukumar ta sanya corticosteroids cikin abubuwan da ba a yarda a yi amfani da su a matsayin bleaching agents ba, tare da mercury da mercury compounds. Wannan ba yana nufin cewa duk wani corticosteroid cream ba shi da amfani ba ne; akwai lokutan da likita kan rubuta su domin magance wata cutar fata. Abin da ke da matsala shi ne mayar da irin waɗannan magunguna kayan haskaka fata ko amfani da su ba tare da kulawar ƙwararre ba.

By ukarofi

Leave a Reply