Mutum uku sun rasu yayin rige-rige a gidan gwamnatin Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Aƙalla mutane uku ne suka rasu yayin da wasu da dama suka jikkata a lokacin da suke rige-rige shiga gidan Gwamnatin Jihar Neja da ke Minna. Waɗanda suka jikkatan a halin yanzu suna karɓar magani a Babban Asibitin Minna.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a daren Talata wayewar Laraba a lokacin da aka gayyaci wasu dandazon matasa zuwa gidan gwamnatin domin lallashin su akan janye batun zanga-zangar da aka alaƙanta da mutuwara masu haƙar ma’adinai 37 a jihar.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai wata mata ‘yar gudun hijira mai suna Dije da ‘yarta Hurairat daga ƙauyen Allawa da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro. A shekarar 2023 ne ‘yan bindiga suka suka halaka mijin Hurairat mai suna Abubakar, a hanyar Allawa zuwa Pandogari.

Majiyoyi ciki har da waɗanda na hannun daman gwamnan ne sun ce gabanin dandazon, matasan sun taru da gidan gwamnatin ne domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Mohammed Umaru Bago.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ta shaida wa manema labarai cewa, wasu mutane ciki har da mata sun cika gidan gwamnatin a lokacin da suka ji cewa gwamnan zai raba wa matasan N10,000 kowanne.

Gwamnati ko rundunar ‘yan sandan jihar ba su fitar da wani rahoto ba a kai yayin haɗa wannan rahoto.

By Babaji

Leave a Reply