Ba za mu amince da ƙudirin INEC Na amfani da AI a zaɗen 2027 ba – Obidient Movement 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

ƙungiyar Obidient Movement ta yi watsi da shirin Hukumar INEC na amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) a babban zaɗen shekarar 2027.

ƙungiyar ta ce bai kamata INEC ta fara amfani da sabuwar fasaha ba, alhali har yanzu ba a magance wasu muhimman matsaloli da suka shafi sahihancin zaɗe, bayyana sakamako da yadda ake tura sakamakon zaɗe ba.

A wata sanarwa da sashen yada labarai da sadarwa na ƙungiyar ya fitar, Obidient Moɗement ta bayyana damuwa kan abin da ta kira rashin bayyana gaskiya da kuma zargin akwai alaƙa tsakanin INEC da jam’iyyar APC mai mulki.

ƙungiyar ta ce matsalar zaɗen Nijeriya ba fasaha ba ce kawai, sai dai yadda hukumomin da ke gudanar da zaɗe suke aiki, da kuma yadda suke tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

Ta buƙaci INEC ta fara bayyana yadda aka magance matsalolin da suka taso a zaɗukan baya kafin ƙara amfani da sabbin fasahohi.

Obidient Movement ta kuma tambayi INEC yadda za a yi amfani da AI a zaɗen 2027, matsalolin da ake son fasahar ta magance da kuma matakan kariya da za a ɗauka domin hana amfani da ita ba bisa ƙa’ida ba.

ƙungiyar ta kuma ambaci wani bincike na Mundɗ Analytics, wanda ta ce ya yi zargin cewa an loda sakamakon shugaban ƙasa daga rumfunan zaɗe sama da 50,000 a zaɗen 2023 ta wayoyin hannu.

Sai dai ƙungiyar ta yi wasu zarge-zarge kan wasu jami’an INEC da hannu a magudin zaɗe, ba tare da gabatar da wata shaida mai zaman kanta da za ta tabbatar da waɗannan zarge-zargen a cikin sanarwar ba.

ƙungiyar ta buƙaci INEC ta Fitar da cikakken tsarin gudanar da zaɗen 2027, ciki har da fasahohin da za a yi amfani da su da matakan kariya.

Gudanar da bincike mai zaman kansa kan tsarin fasahar zaɗe na INEC, tare da bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

Tabbatar da cewa ana tura sakamakon zaɗe cikin hanya mai gaskiya kuma za a iya tantancewa.

Bayyana dalla-dalla yadda za a yi amfani da AI tare da gwada fasahar kafin amfani da ita a zaɗe.

ɗaukar matakan da za su tabbatar da ’yancin sashen fasahar sadarwa na INEC daga tsoma bakin siyasa.

Obidient Movement ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na yin magudi a zaɗen 2027 na iya haifar da fushin jama’a da rikicin zaɗe.

Ta buƙaci shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, da ya sake duba tsarin hukumar tare da ɗaukar matakan da za su ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kan sahihancin zaɗen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply