Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayyana cewa, mutumin da aka tsinci gawarsa a ƙarƙashin Gadar Katampe dake kan babban titin zuwa Kubwa ya mutu ne akan wata matar aure a wani otel da ke Gwarimpa.
Kwamishinan ’Yan Sandan FCT, Ahmed Muhammed Sanusi, ne ya bayyana hakan ranar Asabar a Abuja yayin da yake yi wa ’yan jarida bayani kan binciken da rundunar ta gudanar game da gawar mutumin.
Sanusi ya ce tun kafin a tsinci gawarsa, iyalan mamacin sun kai rahoton cewa ya ɓace.
Ya ce an gano gawarsa da misalin ƙarfe 9:00 na safe ranar 26 ga watan Agusta a ƙarƙashin gadar Katampe.
A cewarsa, binciken ’yan sanda ya gano cewa mutumin ya yi magana da wata Mrs Rukayat Muhammed da ke Garki Area 2 kafin ɓacewarsa, inda ya ce ana zargin tana cikin wata alaƙar soyayya da mamacin.
Kwamishinan ya ce mamacin da Muhammed sun sauka a Good Samaritan Guest House da ke 2nd Avenue, Gwarimpa, inda matar ta gano cewa mutumin ya daina numfashi.
Sai dai maimakon ta kai rahoton lamarin ga ’yan sanda, Sanusi ya ce matar ta ɗauki wayar mamacin ta bar otel ɗin.
Ya ce wayar ta zama muhimmiyar shaida a binciken, bayan jami’an ’yan sanda sun gano mutumin da mamacin ya yi magana da shi na ƙarshe.
“Binciken ya kai ga Mrs Rukayat Muhammed ta Garki Area 2, wadda aka gano tana cikin wata alaƙar soyayya da mamacin, kuma ta adana lambarsa a wayarta da sunan ‘Safiyat’,” inji kwamishinan.
Sanusi ya ce matar ta shaida wa masu bincike cewa ta gano mamacin ba ya numfashi kuma ya mutu.
Ya ƙara da cewa, bayan wasu sa’o’i, jami’an otal ɗin sun yi ƙoƙarin tuntuɓar mutanen da ke cikin ɗakin amma ba su samu amsa ba, kafin daga bisani aka shiga ɗakin inda aka gano gawar.
Kwamishinan ya ce daga nan ne wasu ma’aikatan otel ɗin biyu, Ibrahim Omeiza da Kefat Bitrus, suka cire gawar daga ɗakin.
Ya ce mutanen biyu sun ɗauki gawar suka kai ta yankin Kubwa Eɗpressway, kusa da ƙarƙashin Gadar Katampe, inda suka jefar da ita a bakin hanya, da alama domin nesanta otel ɗin da shugabanninsa daga lamarin.
Sanusi ya ce, “Bincikenmu ya nuna cewa maimakon su kai rahoton gano gawar ga ’yan sanda, ma’aikatan otel ɗin biyu, Ibrahim Omeiza da Kefat Bitrus, sun cire gawar daga ɗakin, suka kai ta Kubwa Eɗpressway kusa da ƙarƙashin Gadar Katampe, inda suka jefar da ita a bakin hanya.”
Gano gawar ya jefa mazauna yankin cikin fargaba, inda rahotannin farko suka danganta lamarin da fashi da makami irin na “one chance” ko kuma satar mutane.
Sai dai Sanusi ya ce rundunar ba ta dogara da hasashe ba, inda ta fara gudanar da cikakken bincike bayan iyalan mamacin sun kai rahoton ɓacewarsa.
Ya ce daga baya masu binciken suka tabbatar cewa mutumin da aka tsinci gawarsa ƙarƙashin gadar shi ne wanda iyalansa suka kai rahoton ɓacewarsa.
Sai dai kwamishinan ya jaddada cewa har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutumin da kuma cikakkun yanayin da mutuwar ta faru.
“Bari in bayyana a sarari cewa har yanzu ana ci gaba da bincike. Ainihin musabbabin mutuwar mamacin da kuma yanayin da mutuwar ta faru har yanzu suna ƙarƙashin bincike,” inji shi.
Sanusi ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da wasu matakan bincike domin gano cikakken bayani game da mutuwar.
Ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka gano yana da hannu wajen mutuwar mutumin ko kuma ɓoye gawarsa da jefar da ita, zai fuskanci hukuncin doka.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a da su guji ɓoye bayanan da za su taimaka wajen bincike ko kuma hana jami’an ’yan sanda gudanar da aikinsu, yana mai cewa doka za ta ɗauki mataki kan duk wanda aka samu da laifi.
