Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta amince da wani cikakken shiri na zamanantarwa da inganta tashoshin jiragen ruwa na Onne, Ribas, Delta da Kalaba, a wani mataki da ta ce zai ƙarfafa ababen more rayuwa na harkokin ruwa, inganta sauƙin kasuwanci da kuma mayar da Nijeriya cibiyar jigilar kayayyaki ta duniya a Afirka.
Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Gboyega Oyetola, ne ya bayyana amincewar a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026. Oyetola ya bayyana amincewar a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen aiwatar da ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce wannan amincewa ta biyo bayan wadda gwamnatin ta bayar a baya domin gyara da inganta tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Tin Can Island da ke Jihar Legas. A cewarsa, matakin wani ɓangare ne na ƙudurin gwamnati na gina tsarin tashoshin jiragen ruwa na ƙasa mai daidaito da kuma iya gogayya da sauran ƙasashe a duniya.
Ministan ya ce faɗaɗa shirin zamanantar da tashoshin jiragen ruwa zuwa wajen Legas zai taimaka wajen rage cunkoson jigilar kayayyaki a wannan cibiyar kasuwanci, tare da samar da wasu ƙofofin shiga da fita na ƙasa da ƙasa masu inganci. Ya bayyana cewa inganta ababen more rayuwa a tashoshin Onne, Ribas, Delta da Kalaba zai ƙara ƙarfin karɓa da sarrafa kayayyaki, rage lokacin da jiragen ruwa ke ɗauka kafin su kammala ayyukansu a tashar, da inganta alaƙar kasuwanci tsakanin yankuna.
Haka kuma, zai taimaka wajen rage kuɗin jigilar kayayyaki daga wannan sashe na ƙasar zuwa wani. Oyetola ya ƙara da cewa waɗannan tashoshin jiragen ruwa suna da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da masana’antu a Nijeriya, don haka akwai buƙatar samar musu da kayan aiki da ababen more rayuwa da za su dace da buwatun tattalin arzikin ƙasar da ke ci gaba da haɓaka.
Ya ce shirin inganta tashoshin yana cikin wani babban tsari na faɗaɗa ababen more rayuwa na harkokin ruwa, wanda ya haɗa da amincewar Gwamnatin Tarayya ga bunƙasa sabbin tashoshin ruwa masu zurfin gaske na Ibom, Bakassi, Agge, Gateway, Ondo da Bonny.
Ministan ya ce, tsarin gwamnati ya shafi dukkan ɓangarorin harkokin ruwa, inda ake zamanantar da tashoshin da ake da su tare da sauƙaƙa samar da sababbin tashoshin ruwa masu zurfin gaske. Ya ce haɗin gwiwar waɗannan jarin zai faɗaɗa ƙarfin Nijeriya a fannin harkokin ruwa, samar da manyan hanyoyin bunƙasar tattalin arziki, tare da ɗaga darajar ƙasar zuwa matsayin babbar cibiyar harkokin ruwa da jigilar kayayyaki a Afirka.
Oyetola ya kuma ce burin gwamnati shi ne samar da ingantaccen tsarin harkokin ruwa da jigilar kayayyaki, inda tashoshin jiragen ruwa, hanyoyin mota, layin dogo, hanyoyin ruwa na cikin gida da sauran ababen sufuri za su kasance cikin haɗin kai domin tabbatar da zirga-zirgar kayayyaki cikin sauƙi.
A cewarsa, gwamnati na son rage lokacin da ’yan kasuwar Nijeriya ke kashewa wajen jigilar kayayyaki, tare da rage kuɗaɗen da suke kashewa, domin samar da yanayin da zai ƙarfafa saka jari da kuma samar da guraben ayyukan yi.
Ministan ya ce Ma’aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Bahaushe za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatocin jihohi, masu gudanar da tashoshin jiragen ruwa, masu zuba jari, kamfanonin jigilar kayayyaki ta ruwa da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da cewa ayyukan sun haifar da ɗorewar amfani ga Nijeriya da tattalin arzikinta na ruwa.
Ya ƙara da cewa idan Nijeriya ta samu ingantattun ababen more rayuwa, manufofi masu kyau da kuma yanayin saka jari mai kyau, ƙasar na da damar zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin harkokin ruwa da jigilar kayayyaki a Afirka.
