Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Dakta Aminu Wada Maida, ya bayyana cewa ’yan Nijeriya sun yi amfani da data na intanet da suka haura terabyte miliyan 1.66 cikin shekara guda.
Dakta Maida ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Otel ɗin Onomo Allure da ke Abuja, yayin bikin buɗe taron kwanaki biyu na dandalin Nijeriya kan Haɗin Kan Dijital da Zuba Jari, wanda Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta shirya tare da haɗin gwiwar SwedFund da Okla.
Ya ce adadin ya nuna cewa amfani da intanet a Nijeriya ya ƙaru da kashi 47 cikin 100, idan aka kwatanta da terabyte miliyan 1.33 da ’yan Nijeriya suka yi amfani da su a shekarar da ta gabata.
Saboda wannan ƙarin amfani da data ta intanet, Mataimakin Shugaban NCC ya ce Nijeriya na buƙatar ci gaba da zuba jari da faɗaɗa hanyoyin sadarwa domin inganta ƙwarewar masu amfani da harkokin sadarwa a ƙasar.
Taken taron shi ne, “Buɗe ƙofofin Zuba Jari a Ababen More Rayuwa ta hanyar Bayanai, Bayyananniyar Harkar Aiki da Hacin Gwiwa.”
Dakta Maida ya ce an shirya taron ne a daidai lokacin da Nijeriya ke bikin cika shekaru 25 da fara amfani da tsarin GSM, yana mai cewa sauye-sauyen manufofi da kuma tsarin bayar da lasisi cikin gaskiya da bayyana komai sun ƙarfafa gwiwar masu zuba jari masu zaman kansu wajen shiga harkar sadarwa.
A cewarsa, taron ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin damar tattaunawa a fili tare da samar da shawarwari masu ƙarfi da za su taimaka wajen ciyar da harkar sadarwa gaba, daidai da ajandar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta gina tattalin arzikin Nijeriya mai darajar dala tiriliyan ɗaya.
Ya ce NCC na ci gaba da ɗaukar matakai domin inganta yanayin zuba jari a fannin sadarwa, tare da aiwatar da nauyin da aka ɗora mata na kare haƙƙin masu amfani da sabis da kuma tabbatar da adalci a gasar da ake yi tsakanin kamfanonin sadarwa.
Dakta Maida ya ce, “Mun kasance muna aiki domin inganta yanayin zuba jari. Daidaita farashin sabis na sadarwa da aka yi a shekarar 2025 ya taimaka wajen magance matsalolin kuɗi da ke fuskantar kamfanonin sadarwa da kuma ƙarfin da suke da shi na ci gaba da zuba jari, tare da kyakkyawan fata cewa masu amfani za su samu ingantaccen sabis.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana ababen more rayuwar sadarwa a matsayin Muhimman Ababen More Rayuwa na Data na ƙasa, matakin da ya ƙara ƙarfafa tushen kariyar waɗannan kadarori.
