Hadiza Liman ta fice daga APC zuwa NDC a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wata jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, Hajiya Hadiza Liman, ta sanar da ficewarta daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC).

Hajiya Hadiza ta sanar da ficewarta yayin da take magana da manema labarai a gidanta da ke Gusau.

A cewarta, ita da magoya bayanta sama da mutum 10,000 daga ƙananan hukumomi 14 sun bar APC sun koma NDC.

Ta nuna rashin gamsuwarta da abin da ta bayyana a matsayin sakacin Gwamna Dauda Lawal, tana mai cewa sun ba da cikakken goyon bayansu lokacin da suke cikin Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a lokacin da ya zama Gwamna a 2023.

“Tun lokacin da muka bi Gwamna Dauda Lawal daga PDP zuwa APC, Gwamna Dauda Lawal ya kasa kula da mu,” in ji ta.

Hajiya Hadiza Liman ta bayyana ɗan takarar Gwamna na NDC, Sanata Kabiru Garba Marafa, a matsayin jam’iyyar da za ta tabbatar da nasara a zaɓen 2027 a jihar.

Ta yi kira ga mutanen jihar Zamfara da su bai wa Sanata Kabiru Garba Marafa goyon bayansu don cimma nasara a zaben da ke tafe a jihar.

“Daga yau ina sanar da ɗimbin masoyana da magoya baya na cewar na ba fita daga Jam’iyyar APC, na koma Jam’iyyar NDC a Jihar Zamfara”. Cewar Hajiya Hadiza Liman.

By ukarofi

Leave a Reply