
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (NRS) da aka sani da FIRS, ta yi watsi da wani saƙon ɗaukar aiki da ke yawo a kafafen sada zumunta da sunan Federal Inland Revenue Service (FIRS), inda ta bayyana shi a matsayin “damfara”.
A wani saƙo da ta fitar wa al’umma mai taken “Fraudulent Recruitment Notice” da ta wallafa a sahihin shafinta na X.com a ranar Litinin, NRS ta ce ta samu labarin saƙon bogi da ake yaɗawa a kafafen Soshiyal Mediya mai taken “Federal Inland Revenue Service – Replacement”.
A cewarta, saƙon yana tallata batun damarmakin ɗaukar aiki a hukumar tare da kira ga masu muradin aiki da ita da su aike da bayan shaidar karatunsu ta adireshin Imel kamar haka: [email protected]. Akan haka ne ta nesanta kanta da shi tare da bayyana cewa ba daga gareta ba ne hasali ma hanyar damfara ce da ake ƙoƙarin amfani da ita wajen cimma wata manufa da ka iya jefa al’umma cikin haɗari.
Hukumar ta kuma ankarar da jama’a cewa an maye gurbin FIRS da NRS don haka su kiyaye tantancewa musamman wajen neman wani bayani da ya shafi harkokinsu na yau da kullum. NRS ta kuma ce ba ta sahalewa kowane irin ɗaukar aiki ba a yanzu daga gare ta kai-tsaye ko kuma a madadinta ta hanyar samun ‘yan shiga tsakani.
Kazalika, ta shawarci jama’a da su ƙaurace wa saƙon da kuma kulawa wajen amsa wa saƙonni ko adireshin da suka shafi ɗaukar aiki, tana mai cewa za ta sanar da al’umma saƙon ɗaukar aiki ta sahihan shafukanta a lokacin da ya dace.

