Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna dikko ya amince da sabbin naɗe naɗin muƙamai guda bakwai a Katsina.
Sanarwa ɗauke da sa hannun sakataran yaɗa labarai na gwamna Muhammad Kaula, fitaccen malamin addinin musulnci kuma jigo a JIBWIS Sheikh Dr Nasiru Abdulrahaman Funtua ya zama shugaban hukumar alhazai ta Jihar Katsina.
Gwamnan ya Kuma naɗa Dr Sirajo Yakubu Ɓatagarawa wanda tsohon jami’in hukumar DSS da Abubakar Kabir Kusada tsohon jami’i a hukumar wutar lantarki ta ƙasa a matsayin masu bashi shawara.
Haka kuma Muhammad Saifuddeen Yakubu Musa da ga sheik Yakubu Musa Hassan sautus Sunnah ya zama shugaban hukumar HISBAH da Sirajo Wowo a matsayin daga darakta janaral na hukumar kila da zaizayar ƙasa da kwararowar hamada (KEWMA) a Katsina.
Sai Shehu Sanin Dandume da Alhaji Lawal Ibrahim Musa muƙamin babban mataimaki na musamman da mamba na hukumar alhazai ta Jihar Katsina.
Gwamnan Dikko Raɗɗa ya taya murna samun wannan muƙami da kira a gare su da su sanya Jihar Katsina a gaban su da muradin al’umma baki ɗaya.
