
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Laolu Akande, wanda tsohon kakakin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ne, ya musanta wasu kalamai na jigon jam’iyyar (NDC), Babachir Lawal akan ababen da suka faru gabanin zaɓen 2023.
Babachir Lawal, wanda kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) ne daga shekarar 2015 zuwa 2017, marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige shi a muƙamin ne bisa zargin sa da hannu a rashawa.
A wata hira da aka yi da shi a kwanan nan, Babachir Lawal ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari ya ɗauki cewa tsohon mataimakinsa na shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya gwabza da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023 a matsayin bambaraƙwai. Ya ce, da Buhari zai tsinci kansa a halin tsaka-mai-wuya wajen goyon bayan Osinbajo akan Tinubu, wanda tsohon gwamnan na Jihar Legas ne da suke da tsohuwar alaƙa.
A cewarsa, matsayar Buhari ta samu ne bisa tasirin biyayyarsa ga Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin mutumin da ya nemi a zaɓe shi a matsayin shugaba sannan daga baya gaje shi a kujerar. Ya bayyana cewa, Buhari zai ce da Osinbajo zai gwabza da Tinubu a neman kujerar shugaban ko da kuwa yana da cancantar zama a kujerar, da zai samu kansa a halin zullimi da rashin tabbas.
Saidai, a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, Akande, wanda she ne kakakin Osinbajo daga 2015 zuwa 2023, ya bayyana iƙirarin tsohon sakataren a matsayin ƙarya. Ya ce, yana sane da matakan da aka riƙa ɗauka a fadar shugaban ƙasa, musamman waɗanda suka shafi alaƙar da ke tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasar da Buhari.
A cewarsa, “A lokuta mabambanta guda huɗu, an yi wa Buhari tayi na musamman ya goyi bayan Tinubu, yana faɗa masa kai-tsaye: ‘idan ban goya maka baya ba, wa zan goya wa?'” Ya bayyana cewa, Buhari ya kuma yaba wa yaƙin neman zaɓen Osinbajo a fili yayin zaɓukan fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2022. Ya kuma nuna goyon bayansa a gaban baki ɗaya ‘yan kwamitin.
