Shekaru 35 ban taɓa karɓar alawus na tsohon gwamna ba – Garkuwan Yauri

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Tsohon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kebbi Alhaji Abubakar Musa (Garkuwan Yauri) ya bayyana cewa tun lokacin da ya bar gwamna a jihar Kebbi shekaru talatin da biyar da suka wuce ba a taɓa ba shi wani alawus ba a matsayin sa na tsohon gwamna.
Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da tashar JDK Media ranar Litinin ɗin nan.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba a taba gayyatar sa ko neman wata shawara ba kan lamurran gwamnatin jihar Kebbi ko taron dattijawan jihar Kebbi a ke yi ba a taɓa gayyatar sa hasali ma bai taɓa ganin Gwamnan jihar Kebbi ba a matsayin gwamna ba amma ana gayyatar sa a jihar Sokoto, musamman ko lokacin da za a rantsar da gwamnoni sukan gayyace shi kuma suna mutunta shi.

Ya bayyana cewa irin wannan abin yana da nasaba da ƙyashi saboda a cewar sa, waɗansu suna ganin don me za a bai wa wane abu kaza?
“Kana da masaniyar tun lokacin da na bar Gwamna a Kebbi ba a taba ba ni wani alawus ba a matsayina na tsohon gwamna yau shekaru talatin da biyar amma sauran wadanda muka yi mulki tare na wadansu jihohi suna karba” inji shi.
Ya bayyana cewa duk da ya ke dai yaran sa ne musamman Adamu Aliero da mu ne muka dauke shi aiki da kuma Sai’du Nasamu Dakingari.
Ya bayyana cewa akwai lokacin da Aliero yana neman a sake zaɓen sa karo na biyu amma ya ya ji tsoron zuwa wadansu garuruwa sai da ya biyo ta wajena na yi masu magana sannan suka bar shi ya shiga garin su.

By ukarofi

Leave a Reply