Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta kama wasu ’yan uwa biyu da wani da ake zargi da yin maganin gargajiya, bisa zargin tono kaburbura tara da cire kawunan gawarwakin da aka binne a cikin su, a garin Omupo da ke ƙaramar Hukumar Ifelodun ta jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kwara, Ojo Adekimi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake yi wa manema labarai bayani a hedikwatar rundunar da ke Ilorin, lokacin da aka gabatar da wasu da ake zargi da aikata laifuffuka da kuma masu hannu a ayyukan tsafi. Adekimi ya ce, lamarin ya fara bayyana ne a watan Mayun 2026, lokacin da wasu mazauna yankin suka je maƙabarta domin binne wani mamaci, sai suka gano cewa an tono kaburbura da dama, kuma an cire kawunan gawarwakin da ke cikin su. Ya bayyana cewa, an kama waɗanda ake zargin, waɗanda aka bayyana sunayensu da Abu Jimoh, Ayo Jimoh da Mukaila Bello, bayan gudanar da bincike bisa bayanan sirri da jami’an tsaro suka tattara.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce an kama ’yan uwan biyu ne a ranar 8 ga Oktoba, da misalin ƙarfe biyar na safiya, a lokacin da ake zargin suna ƙoƙarin tono wani kabari a maƙabartar. A cewarsa, ’yan’uwan sun amsa zargin aikata laifin yayin da ake yi musu tambayoyi, sannan suka ambaci Mukaila Bello, wanda ake zargi da yin maganin gargajiya, a matsayin mutumin da ya sayi sassan jikin gawarwakin da aka cire.
Sai dai Adekimi ya ce har zuwa lokacin da yake magana, rundunar ba ta gano ko kwato sassan jikin da ake zargin an cire ba. Ya ce, “Mun gano cewa an tono kaburbura kusan tara, kuma an cire kawunan gawarwakin da ke cikinsu. An kama mutanen uku, amma har yanzu ba mu gano sassan jikin da ake zargin sun cire ba.”
Kwamishinan ya ƙara da cewa, an cafke ’yan uwan ne a lokacin da ake zargin suna ƙoƙarin tono wani kabari, inda ya bayyana cewa ɗaya daga cikinsu yana da nakasar jiki. Sai dai ɗaya daga cikin ’yan’uwan da aka kama, Ayo, ya musanta hannu a laifin, yana mai cewa bera ne ya shiga maƙabartar suke bi lokacin da aka kama su. A cewarsa, babban ɗan uwansa ne yake bin beran da ya shiga makabartar, inda ya tsallake wani ɗan ƙaramin katanga ya bi shi ciki, kafin daga bisani ya fara haƙa ƙasa a wani kabari. Ayo ya ce, “ɗan uwana ne yake bin wani bera da ya shiga makabartar. Ya tsallake ƙaramin katangar ya shiga bin beran, sannan ya fara haƙa kabarin. Ina gaya masa ya bar wurin, amma kuskuren da na yi shi ne na je inda yake.”
Ayo, wanda ya ce yana da shekaru sama da 50 kuma ɗan asalin unguwar Ile Fayabale ne da ke Omupo, ya dage cewa ba shi da hannu a zargin cire kawunan gawarwakin.
Babban ɗan uwansa, Abu, ya bayar da irin wannan bayani, inda ya ce suna kan hanyarsu ta zuwa gona da safe ne suka ga wani bera ya shiga maƙabartar, sannan ya ɓuya a cikin wani kabari. Ya ce babban ɗan uwansa ne ya ja hankalinsa kan beran, amma ya gargaɗe shi cewa bin dabbar cikin makabartar na iya jefa su cikin matsala idan aka gan su suna yin irin wannan abu.
A nasa ɓangaren, Mukaila Bello, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai maganin gargajiya da ke zaune a Ajase-Ipo, ya amince cewa ya san ’yan’uwan biyu, amma ya musanta zargin sayen sassan jikin mutane daga wurinsu. Bello ya ce hulɗarsa da ’yan uwan ta tsaya ne kawai kan sayen itace daga gare su, yana mai cewa bai san komai game da zargin cire sassan jikin gawarwaki ba. Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike kan lamarin.
