Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sanar da sabbin matakan zamanantar da ɓangaren shari’a na jihar, ciki har da amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan kotuna, shari’o’in da za a gudanar ta yanar gizo, inganta samar da wutar lantarki da kuma ƙara inganta walwalar jami’an shari’a.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin buɗe sabon shekarar shari’a ta 2026/2027 na babbar kotun shari’a ta Jihar Katsina, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na Justice Umaru Abdullahi Auditorium da ke Katsina.
A jawabinsa ga jami’an shari’a da sauran masu ruwa da tsaki, Gwamna Raɗɗa ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da ’yancin ɓangaren shari’a, bin doka da oda, da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori uku na gwamnati.
Gwamnan ya ce: “Ɓangaren shari’a yana da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da bin doka da oda da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyyarmu. A matsayinsu na abokan tafiyar gwamnati, ɓangaren zartarwa, majalisa da shari’a dole ne su ci gaba da yin aiki tare bisa iyakokin nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora wa kowannensu.”
Ya tabbatar wa ɓangaren shari’a cewa gwamnatinsa ba za ta tsoma baki cikin ayyukan kotuna wajen gudanar da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu ba, yana mai jaddada ƙudirin samar da yanayin da zai ba kotuna damar gudanar da shari’a cikin adalci ba tare da nuna son kai ba.
Dangane da zamanantar da ɓangaren shari’a, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa an amince da cikakken shirin sanya kwamfuta da amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan kotuna, ciki har da shari’o’in da za a riƙa gudanarwa ta yanar gizo a hedikwatar babbar kotun shari’a da rassanta da ke Funtua, Daura, Malumfashi da Dutsin-Ma.
Ya ƙara da cewa an fara girka na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana a hedikwatar babbar kotun shari’a, domin tabbatar da samun wutar lantarki mai ɗorewa, inganta ayyukan kotuna da kuma hanzarta gudanar da shari’a.
“Mun ƙuduri aniyar amfani da fasaha wajen inganta ayyukan kotunanmu, rage jinkiri da kuma sauƙaƙa wa al’umma samun adalci.”Inji Malam Dikko.
Da yake magana kan ƙalubalen tsaro, gwamnan ya jaddada buƙatar tsarin shari’a ya samar da ingantattun hanyoyin tunkarar laifuffukan yanar gizo, garkuwa da mutane, sace-sace da sauran sabbin nau’ukan aikata laifuffuka.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi gyara ga dokar laifuffuka ta jihar, wato Penal Code, domin fayyace ayyukan masu ba da bayanan sirri ga masu aikata laifuffuka tare da tanadar hukuncin da ya dace a kansu.
Haka kuma, ya bayyana cewa aikin sake duba dokokin Jihar Katsina da sauran ƙananan dokoki da ƙa’idoji ya kusa kammaluwa, tare da sanya su cikin tsarin zamani ta hanyar fasahar dijital, domin tabbatar da cewa dokokin jihar sun dace da sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewar al’umma na wannan zamani.
Dangane da jin daɗin jami’an shari’a, Gwamna Raɗɗa ya sanar da cewa an samar wa alƙalan babbar kotun shari’a filayen gina gidaje masu kyau da kuma alawus na musamman, domin taimaka musu wajen gina gidajen kansu.
Ya kuma bayyana cewa ana shirye-shiryen sauya motocin gwamnati da suka cancanci sauyawa, tare da samar da lamunin sayen motoci ga alƙalan kotunan majistare. Ya ce akwai shirin faɗaɗa wannan tsari zuwa ga alƙalan kotunan Shari’a da Kadis
Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa an kafa kotuna na musamman domin inganta warware taƙaddamar kasuwanci, karɓo kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma kare muhalli.
A nasa jawabi,babban jojin Jihar Katsina Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ya sanar da cewar a shekarar da ta gabata zuwa yanzu sun saurari shari’o’i guda 86.
