ZSUBEB za ta dasa bishiyoyi a makarantu 70 a ƙananan hukumomi 14

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Hukumar bada Ilimi ta bai ɗaya ta jihar Zamfara (ZSUBEB) ta ƙaddamar da shirin Greening Schools and Climate Change Education Initiative (GSCCEI) na dashen itatuwa a ƙaramar hukumar Maradun a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin inganta muhalli mai ɗorewa a makarantu.

Shirin, shugaban hukumar, Farfesa Nasir Garba Anka ya kaddamar.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ibrahim Musa Maizare a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an tsara shirin ne domin ƙarfafa dasa bishiyoyi da kuma ƙarfafa ilimin sauyin yanayi a makarantu da al’ummomi a faɗin Jihar Zamfara.

Shugaban hukumar, wanda daraktan ayyukan ilimi, Alhaji Garba Abdullahi ya wakilta, ya ce manufar shirin ita ce samar da yanayi mai dacewa na koyo da kuma inganta ɗorewar muhalli.

Ya bayyana cewa dasa bishiyoyi ba wai kawai zai taimaka wajen inganta yanayin makaranta da kare yanayi ba, har ma zai wayar da kan ɗalibai da al’umma kan buƙatar kiyaye muhalli.

A cewarsa, yaƙin dasa bishiyoyin zai bazu zuwa dukkan ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.

Ya ce makarantu biyar da aka zaɓa a kowace ƙaramar hukuma ne ake sa ran za su amfana da shirin, wanda jimillarsu ta kai makarantu 70.

Ya bayyana cewa kowace makaranta da ta amfana za ta samu nau’ikan tsiron bishiyoyi guda goma.

Don haka ya bukaci makarantun da al’ummomin da suka amfana da su kula da tsirran yadda ya kamata domin tabbatar da rayuwarsu da amfaninsu na dogon lokaci.

A nasa jawabin, Sarkin Maradun, Alhaji Garba Muhammad Tambari, wanda Sarkin Gabas, Alhaji Muhammad Sani ya wakilta, ya yaba wa hukumar ta ZSUBEB kan ɓullo day wannan shiri.

Ya bayyana shi a matsayin wani tsari na shiga tsakani wanda yazo kan lokaci, yana mai jaddada cewa shirin zai taimaka wajen kare muhalli da inganta tsarin koyarwa cikin kwanciyar hankali a tsakanin malamai da ɗalibai.

By ukarofi

Leave a Reply