Daga UMAR GARBA a Katsina
Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su fifita jin daɗin ‘yan ƙasa, yana mai cewa ya kamata a auna shugabanci ta hanyar tasirinsa ga rayuwar mutane.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin darakta janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu da tawagarsa a faɗarsa da ke Katsina.
Ya yi gargaɗi ga ‘yan siyasa game da cin mutunci, zagi da mugunta, yana mai cewa ya kamata su nemi amincewa da goyon bayan jama’a.
“Siyasa ba hauka ba ce. Idan kana son mutane su bi ka, dole ne ka shawo kansu. Ba sai ka yi cin mutunci ko zagi ko mugunta ba don cimma burinka na siyasa,” in ji shi.
Da ya ke ambaton ayoyi daga Alqur’ani, sarkin ya buƙaci shugabannin siyasa da su rungumi tawali’u, rashin son kai da tausayi, yana mai jaddada cewa shugaba ya kamata ya yi wa mutane hidima maimakon inganta muradun kansu.
Ya ce dimokuraɗiyya ta buƙaci shugabanni su sanya buƙatun ‘yan ƙasa gaba wajen yanke shawara da kuma tabbatar da cewa manufofin jama’a sun nuna buƙatunsu da burinsu.
Sarkin ya kuma nuna damuwa game da lalacewar tarbiyyar al’umma da ɗabi’u marasa kyau, yana mai kira ga shugabanni akan su gudanar da mulki cikin gaskiya da riƙon amana
Sarkin ya ce, rashin cika alƙawura yayin yaƙin neman zaɓe ya rage amincewar da jama’a ke da shi ga mulkin dimokuraɗiyya, yana mai kira ga ‘yan siyasa da su cika alkawuran da suka ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe.
Sarkin ya kuma yi kira ga dattawan Arewa da su faɗi gaskiya ga masu riƙe da muƙamai da shugabannin siyasa, ba tare da la’akari da alaƙar da ke tsakaninsu ba.
Ya ce yankin Arewa yana buƙatar shugabanni da za su jawo hankali don magance ƙalubalen zamantakewa da tattalin arziki maimakon yin shiru idan masu riƙe da madafun iko sun yi ba dai dai ba.
