Kungiyar direbobin tifa ta gudanar da taron haɗin gwiwa da NARTO a Kano

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Kungiyar Direbobin Tifa ta ƙasa, reshen Jihar Kano da ke yankin Yanrake, ta gudanar da taron haɗin gwiwa da ƙungiyar direbobi ta NARTO, da nufin haɗa kai wajen ƙara wayar da kan masu sana’ar tuƙi a jihar.

An shirya taron ne domin haɗa kai da kuma wayar da kan direbobi kan bin dokokin tuƙi a kan tituna, musamman amfani da tamfol wajen rufe kayan da suka ɗauko.

Da yake jawabi a wajen taron, Sakataren ƙungiyar ta ƙasa, reshen Jihar Kano, Sharu Maikudi Dala, ya ce manufar taron ita ce nuna wa direbobi amfanin bin dokokin tuƙi a kan tituna, tare da amfani da tamfol wajen rufe kayan da suka ɗauko domin guje wa aukuwar haɗurra.

Ya ce ya kamata direbobin tifa su riƙa amfani da tamfol, ganin irin haɗarin da kayan da suke ɗauka ke haifarwa, musamman yashi da duwatsu, waɗanda a wasu lokuta suke zubewa a ƙasa yayin da motocin ke tafiya.

Sharu Dala ya kuma yi kira ga direbobin da su riƙa ba jami’an tsaro haɗin kai yayin gudanar da ayyukansu a kan tituna domin inganta sana’arsu.

Ya bayyana fatan cewa za su yi amfani da abubuwan da aka nuna musu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Shi ma shugaban ƙungiyar direbobin tifa ta reshen Yanrake, Alhaji Murtala Dahiru, ya ja hankalin direbobin kan su guji tuƙin ganganci a kan manyan tituna, wanda kan jawo asarar dukiyoyi, wasu lokuta har ma da rayuka.

Ya ce babban ƙalubalen da ƙungiyar ke fuskanta shi ne korafe-korafen da take samu daga al’umma kan tuƙin ganganci da wasu ’yan ƙungiyar ke yi.

Ya kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Kano da ya taimaka musu wajen samar da filin ajiye motocinsu na dindindin, yana mai cewa ba su da filin kansu da suke ajiye motocin.

Ya koka da cewa wasu mutane suna zuwa suna yi musu barazanar korarsu daga wurin da suke ajiye motocin a yanzu. Ya ƙara da cewa idan aka kore su daga wurin, ba su da wani wuri da za su koma domin gudanar da sana’arsu.

An tattauna muhimman batutuwa da za su taimaka wa direbobin wajen gudanar da sana’arsu. Mahalarta taron sun bayyana gamsuwarsu da yadda aka gudanar da shi, tare da ba da tabbacin cewa za su yi amfani da abubuwan da suka koya.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar na rassa daban-daban, jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa, wakilin Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) da jami’an tsaro.

An gudanar da taron ne a filin ƙungiyar da ke Yanrake, a ranar Lahadin da ta gabata.

By ukarofi

Leave a Reply