TCN ta fara gina tashar wutar lantarki mai karfin 120MVA a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da gina tashar wutar lantarki mai ƙarfin 120MVA, 132/33kV a Ƙaramar hukumar Mashi, domin inganta samar da lantarki da bunƙasa tattalin arzikin yankin.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakane yayin bikin aza harsashin gina tashar da kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasa (TCN) ke gudanarwa.

Ya ce tashar za ta taimaka wajen magance matsalar ƙarancin wutar lantarki da katsewar samar da ita a Mashi da yankunan da ke kewaye, tare da inganta kasuwanci, noma da sauran harkokin tattalin arziki.

Gwamnan ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Katsina bisa haɗin gwiwar da suke yi wajen shirin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 10 ta hanyar hasken rana da sauran hanyoyin samar da makamashi.

A nasa jawabin, Ministan Wutar Lantarki, Mista Joseph Tegbe, ya ce za a gudanar da aikin bisa ƙa’idojin inganci, tare da shirin kammala shi nan da 31 ga Maris, 2027. Ya kuma buƙaci masu gudanar da aikin su tabbatar da ingancinsa, tare da kira ga al’umma da su kare shi daga ɓatagari.

Shi kuwa babban daraktan TCN, Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz, ya bayyana cewa tashar za ta ƙunshi taransfoma guda biyu, kowannensu mai ƙarfin 60MVA, wanda jimillarsu za ta kai 120MVA.

Ya ce kammala aikin zai inganta samar da wutar lantarki ga gidaje, wuraren kasuwanci da harkokin noma, tare da samar da damar bunƙasa ƙananan sana’o’i, jawo zuba jari da haɓaka tattalin arzikin yankin.

By ukarofi

Leave a Reply