Ebola: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 15, ta umarci a samar da guraren killacewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta umarci asibitoci a faɗin Nijeriya da su samar da gadaje na musamman domin killacewa da kuma ƙarfafa matakan kariyar kamuwa da cutar Ebola, tana mai gargaɗin cewa wasu jihohi guda 15 ba su bayar da ba’asi ba kan shirye-shiryensu ga al’amarin.

Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Farfesa Muhammad Pate ne ya bayar da wannan umarni a Abuja a ranar Alhamis, yayin ganawa da manema labarai kan matakan da gwamnati take ɗauka na daƙile yaɗuwar cutar acikin al’ummar ƙasa. Ya bayyana cewa, an umarci cibiyoyin lafiya da su samar da wadatattun matakan daƙile cutar da bayar da kariya musamman ga ma’aikatan lafiya.

Da yake bai wa Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (NEC) ba’asi, farfesan ya ce tuni jihohi 21 suka yi hoɓɓasa wajen kimtsa wa tunkarar yiwuwar yaɗuwar cutar a yankunansu, yana mai kira ga sauran 15 da su hanzarta gabatar wa ma’aikatar lafiyar matakan shirinsu. A cewarsa, ana ƙoƙarin tunkarar cutar ne a matakin ƙasa a ƙarƙashin cibiyoyi kamar haka: “Nigeria Centre for Disease Control and Prevention, NCDC, with support from the World Health Organisation, WHO, and the Africa Centres for Disease Control and Prevention, Africa CDC”, kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Ya yi kira ga asibitocin kuɗi da su hanzarta ruwaito labarin samun ɓullar cutar a cibiyoyinsu kuma su kira taron horarwar da bayar da kariya ga ma’aikatan lafiya. Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Tarayya ta sanar da hukumomin birnin tarayya Abuja kuma za ta cigaba da aiki tare da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da cewa asibitocin da ke ƙarƙashinsu sun kimtsa wa tunkarar cutar yadda ya dace.

Kazalika, ministan ya ce ma’aikatan lafiya sun fi sauƙin kamuwa da cutar saboda yadda suke da alaƙa ta kai-tsaye da marasa lafiya, lamarin da ya sa ya zama wajibi a ɗauki matakai masu tsauri domin kula da kariya daga yaɗuwarta acikinsu da ma al’ummar ƙasa baki ɗaya. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da ma’aikatar ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a Abuja ta bakin ministan, bayan samun wata mata mai ɗauke da ita da aka ce ta zo Nijeriya ne daga Uganda. Daga bisani gwamnatin ta ce matar tana samun sauƙi daga cutar yayin da hukumomi suke aiki tuƙuru wajen ganin sun daƙile yaɗuwarta acikin al’umma.

By Babaji

Leave a Reply