Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu da matarsa sun cilla Kaduna domin buɗe yaƙin neman zaɓen APC na 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Asabar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da matarsa, Oluremi Tinubu suka bar Abuja suka nufi Kaduna domin buɗe taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na zaɓen 2027 da ke tafe.

Da fari, dubunnan magoya bayan APC da wasu ‘yan Nijeriya ne suka cika a filin wasa na Ranchers Bees Stadium da ke Jihar Kaduna gabanin isowar Shugaba Bola Tinubu domin buɗe taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar a yau Asabar.

A cewar jaridar The PUNCH, an ga yadda jama’a suka cika a hanyoyin da ke kai mutane zuwa filin yayin da ‘yan APC suka fara zuwa wajen taron tun da misalin ƙarfe 7 na safe. Sannan an ga yadda wasu magoya baya suke rera waƙoƙi da taka rawa a harshen Hausa da Turanci ciki har da “Asiwaju, Uba Sani for Second Term,” “Tinubu Again,” “Tinubu Our Father,” “Speaker Abbas for Tinubu” and “Tinubu Continuity.”

Haka kuma, an ga magoya baya da dama sanye da ƙananan riguna, huluna da hijabai masu ɗauke da hotunan bajen APC, Tinubu da kuma gwamnoninsu musamman na jihohin Kaduna da Kano.

Wannan taro dai shi ne na farko daga cikin gangamin yaƙin neman zaɓe da jam’iyyar ta shirya domin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da ke tafe, inda ake sa ran samun halartar gwamnoni 31, jagororin jam’iyyar da magoya baya su halarci babban taron domin goyon bayan sake zaɓar Tinubu a karo na biyu.

Kazalika, an baza jami’an tsaro na hukumomin tsaro daban-daban a wasu yankuna na musamman domin bayar da kariya ga al’umma da kuma kare kayayyakin gangamin daga hannun ɓata-gari.

By Babaji

Leave a Reply