
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na Shiyyar Afirka, Dakta Mohamed Janabi, ya tabbatar da cewa a yanzu Nijeriya ba ta da wani mai cutar Ebola biyo bayan fitar da matar nan da ke ɗauke da ita zuwa ƙasar Switzerland a yau Litinin.
Janabi ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, inda ya ce Nijeriya za ta cigaba da sanya ido kan halin da mutane 52 da aka wa gwajin cutar suke ciki, yayin da Switzerland za ta kula da matar da kuma bibiyar halin mijinta, wanda shi ne mutum na 53 da aka yi wa gwajin.
Ya ce, an yi jigilar mutane biyun ne a safiyar yau Litinin kuma ya tabbatar da cewa da maras lafiyar da mijinta ‘yan Switzerland ne. A cewarsa, maras lafiyar na cikin halin warkewa a lokacin da tawagogin lafiyar Nijeriya suka yi nasarar mata magani tun daga lokacin da aka gano tana ɗauke da cutar.
A nasa ɓangaren, Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate ya kuma ce an gano alamun samun sauƙi daga maras lafiyar musamman ganin yadda gwaje-gwajen da aka yi mata a baya-bayan nan suka nuna alamun warkewa. Saidai ya ce hakan ba shi ke nuna ta warke baki ɗaya daga cutar ba. Manhaja ta ruwaito cewa, Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wata wallafa a shafinsa na X, inda ya ce, matar tana nan a hayyacinta sannan an fita da ita ne tare da mijinta nata, yayin tabbatar da biyayya ga sharuɗɗan jigilarsu a hukumance.
Janabi ya kuma taya murna ga Gwamnatin Tarayya, ma’aikatan lafiya, ƙwararru kan harkar magani, masu bayar da agajin gaggawa da sauran abokan hulɗa, yana mai bayyana hakan a matsayin babbar nasara. Kazalika, ya ce akwai buƙatar a cigaba da sanya ido da kuma ɗaukar wasu muhimman matakan kariyar ɓullar cutar.
